Hushpuppi: Kotun Amurka ta saka ranar gurfanar da Abba Kyari kan zargin damfara
- Kotun ƙasar Amurka ta sak ranar sauraron shari’ar su Abba Kyari da mutum biyar da ake zarginsu da shiga sarƙaƙiyar damfarar $1.1 miliyan da Hushpuppi ya jagoranta
- Da farko an ɗage karar daga 12 ga watan Oktoba, 2021 zuwa 17 ga watan Mayu, 2022, sannan daga baya aka sake ɗagewa zuwa 11 ga watan Oktoba, 2022
- Hakan ya zo ne ana tsaka da badaƙalar shari'a tsakanin Kyari da kotun tarayya ta Abuja, inda ake tuhumarsa da safarar hodar-iblis
Kotun ƙasar Amurka ta canza ranar gurfanar da Abba Kyari, dakataccen jami'in ɗan sanda da wasu mutumn biyar, bisa zarginsu da shiga sarƙakiyar damfarar $1.1 miliyan da Romon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi ya jagoranta.
Kotun yankin Amurka ta tsakiyan California ta sake canza ranar gufanarwan daga watan Mayu zuwa watan Oktoba, 2022, duba da buƙatar da uku daga cikin waɗanda ake tuhuma tare da Kyari suka shigar, Premium Times ta ruwaito.
Wannan ya zo ne ana tsaka da badaƙala, bayan shigar da ƙarar Abba Kyari a gaban kotun tarayya dake Abuja da NDLEA ta yi, bisa zarginsa da safarar hodar- iblis.
Premium Times ta ruwaito a watan Satumbar shekarar da ta gabata yadda bangarorin suka shigar da buƙatar ɗage sauraran ƙarar don bai wa mutane ukun damar shiryawa shari'ar.
Yayin sauraron ƙarar a 29 ga watan Maris, 2022, Alƙalin Otis Wright ya amince da cewa, ƙin biyawa ɓangarorin buƙatarsu na iya zama sanadin "hana tawagar dake kare kansu isashshen lokacin da ya kamata su shirya wa shari’ar yadda ya da ce."
Ya ƙara da cewa "hakan zai iya haramtawa masu kare kansu cigaba da kare kansa" sannan ya zama dalilin "Haifar da ɗa mai ido ko gazawa wajen yin adalci" idan kotun ta ƙi amincewa da buƙatar ɗage sauraron ƙarar.
Saboda haka ne, Alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar daga 17 ga watan Mayu, 2022, har zuwa 11 ga watan Oktoba, 2022.
"Masu kare kansun za su bayyana a dakin shari'a 5D na kotun tarayya mai lamba 359W, titin farko, Los Angeles na Califonia a ranar 11 ga watan Oktoba, 2022, da karfe 9:00 na safe," bisa umarnin da alkali ya zartar, a kwafin shari'ar da Premium Times ta samu a ranar Juma'a.
Ɗagewa na biyu
Kotun ta sake ɗage ƙarar da sa ranar fara sauraro a 12 ga watan Oktoba, 2021. Bisa buƙatar da ɓangarorin suka shigar, kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 17 ga watan Mayu, 2022, sannan a karo na biyu ta sake maida wa 11 ga watan Oktoba, 2022.
Lauyoyi guda ukun da ke kare waɗanda ake tuhuma, waɗanda suka shigar da buƙatar ɗage karar dukkansu mazauna Amurka ne.
An saki waɗanda ke kare kansu guda ukun - Rukayat Fashola (wacce aka fi sani da Morayo) Bolatito Agbabiaka ( Bolamide), da Yusuf Anifowoshe ( wanda aka fi sani da AJ da Alvin Johnson) tare da belin bayan gufanarwan.
Sauran masu kare kansu - Kyari, Abdulrahman Juma da Kelly Chibuzo Vincent - na wajen Amurka, a cewar hukumomin gurfanarwa na Amurka.
Tawagar masu gurfanarwan sun shirya kammala shari'ar cikin kwanaki shida, duk da har yanzu Kyari da sauran mutane biyun basa nan.
Yayin tabbatar da adalci na shigar da buƙatar ɗage sauraron ƙarar da suka shigar a shekarar da ta gabata, masu shigar da ƙarar sun ce gwamnatin Amurka ta riga ta mika masu hukumar tsaro a kalla 2.31 GB na data, wanda ya ƙunshi 2,707 na fayil mai amfani da wutar lantarki.
Sun ƙara da cewa, masu gurfanarwan suna da a ƙalla shafuka 6,773 na ƙarin binciken da ake sa ran zai samar wa shari'ar.
Asali: Legit.ng