Zulum ya fara azuminsa a garin Mafa, ya raba N76m, kayan abinci ga talakawa sama da 15,000

Zulum ya fara azuminsa a garin Mafa, ya raba N76m, kayan abinci ga talakawa sama da 15,000

  • Kamar yadda ya saba, Gwamna Zulum ya garzaya garin Mafa rabon buhuhunan shinkafa da sukari
  • Cikin mutum sama da 15,000 da suka halarci rabon, kowanne ya tafi gida da buhun hatsi da kuma kudi N5,000
  • Yayinda maza suka samu shinkafa 50kg da Shadda yadi biyar; kowace mace ta samu turmin atamfa da sukari 10kg

Mafa - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya fara azuminsa na watar Ramadana a mahaifarsa, karamar hukumar Mafa dake tsakiyar jihar ta Borno.

Zulum a jawabin da ya saki ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, ya bayyana cewa da kansa ya jagoranci rabawa talakawa buhuhunan kayan abinci.

A cewar jawabin, akalla mutum 15,327 aka rabawa kudi a hannu da buhunanan shinkafa da sukari, da kuma atamfa na dinkin Sallah.

Kara karanta wannan

Jirgin Abj-Kd: Har yanzu bamu san inda mutum 21 suke ba, amma muna gyara jiragen: NRC

Jawabin yace:

"Wadanda suka amfana sun hada da mata 9,313 da Maza 6,014; kowanne cikinsu ya samu N5000 inda aka raba jimillan N76,635,000:00."
"Bayan kudin, kowani magidanci ya samu buhun shinkafa 50kg da Shadda yadi biyar; yayinda kowace mace ta samu turmin atamfa da sukari 10kg."

Kalli hotunan rabon:

Zulum
Zulum ya fara azuminsa a garin Mafa, ya raba N76m, kayan abinci ga talakawa sama da 15,000 Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Ina muku maraba da watar Ramadana, ku baiwa talakawa abinci: Buhari ga Musulman Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya al'ummar Musulman Najeriya murnan ganin watar Ramadana bayan sanarwan Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

A sakon taya murnarsa, shugaba Buhari ya yi kira ga Musulmai su yi amfani da wannan dama wajen ciyar talakawa da marasa galihu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Juma'a, 1 ga watan Afrilu, 2022.

Kara karanta wannan

Ina muku maraba da watar Ramadana, ku baiwa talakawa abinci: Buhari ga Musulman Najeriya

Buhari yace lokacin azumi wani dama ne dake nunawa masu hannu da shuni irin yunwan da talaka ke fama da shi kulli yaumin.

Buhari ya shawarci Musulmai su daina asarar abinci da almubazzaranci yayinda wasu ke fama da yunwa da kunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: