Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaro, billahi lazi zamu dauko Sojin haya: El-Rufa'i ya fusata
- Gwamna Nasir El-Rufa'i ya bayyana bacin ransa kan yadda lamuran tsaro suka tabarbare a jiharsa
- A cewar El-Rufa'i, da gwamnatin tarayya ta bi shawarin da ake bata da mumunan abinda ya faru ranar Litnin bai faru ba.
- El-Rufa'i yace tuni an bayyanawa hukumar NRC ta daina jigilar mutane da daddare amma akayi watsi da shawaran
Abuja - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya lashi takobin dauko Sojin haya yaki da yan ta'adda biyo bayan harin Bam da aka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna ranar Litinin.
El-Rufa'i, wanda yayi jawabi a fusace ya ce gwamnonin jihohin Arewa maso yamma—Katsina, Zamfara, Kebbi, Sokoto— zasu hada kai da shi wajen daukan Sojin hayan idan gwamnatin tarayya taki kawo karshen hare-hare yankin.
Harin Jirgin Ƙasan Kaduna: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai
El-Rufa'i ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa.
Yace:
"Me ya hana har yanzu jami'an tsaro basu je sun kashe su ba? Ina Sojojinmu suke? Shi yasa nazo ganin shugaban kasa."
"Kuma na fadi cewa idan ba'a dau mataki ba, ya zama wajibi kanmu gwamnoni mu kare al'ummarmu ko da zamu dauko sojin haya daga waje ne."
"Idan Sojojinmu sun gaza, billahi lazi, na rantse da Allah zamu yi. Abin yayi kamari."
A cewar El-Rufa'i, da gwamnatin tarayya ta bi shawarin da ake bata da mumunan abinda ya faru ranar Litnin bai faru ba.
Ya yi gargadin cewa idan ba'a dau mataki na gaggawa ba, yan ta'addan zasu iya mamaye kasar gaba daya.
Shugaban UN yayi Allah wadai da harin jirgin kasan Abuja-Kaduna
Shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres yayi Allah wadai da harin da wasu tsagerun yan bindiga suka kai jirgin Abuja-Kaduna, wanda ya haddasa mutuwar mutane da yawa wasu suka jikkata sannan aka yi garkuwa da wasu.
Guterres a wani jawabi jiya, ya tura sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, ya kuma yi fatan samun lafiya ga wadanda suka jigata sannan yayi addu'ar kubutar da wadanda ke hannun miyagun.
Shugaban ya yi kira ga hukumomin tsaro da su zage damtse wajen kamo duk wadanda suke da hannu a wannan ta'addancin.
Asali: Legit.ng