Labari Da Duminsa: An ga watan Azumin Ramadana a Najeriya

Labari Da Duminsa: An ga watan Azumin Ramadana a Najeriya

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar Sa'ad ya sanar da ganin watan Ramadan na shekarar 2022 a Najeriya
  • Sarkin Musulmin ya ce ingantattun rahotanni sun nuna cewa an ga watan a jihohi kamar Sokoto, Yobe, Zamfara, Katsina, Plateau, Kaduna, Kano ds
  • Sa'ad Abubakar ya umurci al'ummar musulmi su tashi da azumi a gobe Asabar su kuma yi amfani da watan don yin addu'ar zaman lafiya da cigaba.

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban kwamitin koli na harkokin addinin musulunci, Muhammad Sa'ad Abubakar ya sanar da ranar Asabar 2 ga watan Afrilu wacce ta yi daidai da ranar 1 ga watan Ramadan ta 1443, wacce ke nuna fara azumin watan Ramadan, rahoton TVC News.

Labari Da Duminsa: An ga watan Azumin Ramadana a Najeriya
An ga watan Azumin Ramadana na 2022 a Najeriya. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ina muku maraba da watar Ramadana, ku baiwa talakawa abinci: Buhari ga Musulman Najeriya

Sultan din ya bada wannan sanarwar ne cikin wata sanarwa ta talabijin da kuma Twitter a shafin NSCIA.

"Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah, Alhamdu Lillah, an ga watan Ramadan na 1443H a wasu garuruwa a Najeriya," a cewar sakon na Twitter.

A cikin sanarwar na talabijin, Sultan ya ce za a fara azumin a ranar Asabar.

Ya ce:

"Bisa ga rahotanni da aka turo mana na ganin watan ramadan 1443. Ranar Juma'a ne karshen watan Sha'aban. Gobe insha Allah, za mu fara azumi bisa koyarwar shari'a."

Jihohin da aka ga watan na Ramadana a Najeriya

Ya kuma ce rahotanni masu nagarta sun nuna cewa an ga wata a Jihohin Sokoto, Yobe, Zamfara, Katsina, Plateau, Kaduna da Kano da wasu.

Sarkin musulmin ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta magance matsalar rashin tsaro da ke adabar kasar domin jin dadin mutanen kasar da cigaba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Anga wata a wasu sassan kasar nan, inji kwamitin ganin wata

Ya bukaci musulmi su yi amfani da watan na Ramadan su yi addu'a ga Allah ya kawo zaman lafiya da cigaba a kasar.

Ina muku maraba da watar Ramadana, ku baiwa talakawa abinci: Buhari ga Musulman Najeriya

A bangarensa, Shugaba Muhammadu Buhari ya taya al'ummar Musulman Najeriya murnan ganin watar Ramadana bayan sanarwan Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

A sakon taya murnarsa, shugaba Buhari ya yi kira ga Musulmai su yi amfani da wannan dama wajen ciyar talakawa da marasa galihu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Juma'a, 1 ga watan Afrilu, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: