Tashin Hankali: An sake gano wani Bam da aka ɗana a Kaduna, awanni bayan warware wani
- Mutane sun sake gano wani abun fashewa a yankin Shanono dake Anguwar Rigasa karamar hukumar Igabi ta Kaduna
- Wani mazaunin yankin ya ce kananan yara ne suka fara gano Bam ɗin a cikin Jarka a wurin da aka ga na jiya Alhamis
- Kakakin rundunar yan sandan Kaduna, Muhammed Jalige, ya ce tunin jami'an warwae Bam suka dira wurin
Kaduna - Mazauna Anguwar Shanono a Rigasa, ƙaramar hukumar Igabi dake Jihar Kaduna sun gano wani abun fashewa da aka dasa (IED) ranar Jumu'a.
Mutane sun gano abun fashewar ne awanni 24 bayan gano wani makamancin wannan kuma duk a yankin dake kusa da tashar Filin jirgi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Bam ɗin farko da aka gano ranar Alhamis, jami'an cire Bam sun samu nasarar warware shi kuma babu wanda lamarin ya shafa.
Wani mazaunin yankin, Tijjani Umar, ya bayyana cewa kananan yara ne suka gano abun fashewar na ranar Jumu'a a cikin Jarka wacce aka rufe da baƙin abu.
Ya ƙara da cewa waɗan da suka aje abun fashewar sun ɗana shi dai-dai kusa da wani Rafi dake yankin Anguwar.
Ya ce:
"An sake aje na yau a wurin da muka gano Bam ɗin jiya, bamu san abin da ke shirin aukuwa a yankin mu ba. Matar yayana ce ta rugo tana faɗa mun yara sun ga wani Bam a Jarka."
Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?
Rahoto ya nuna cewa tuni aka ƙara jibge jami'an tsaro a yankin domin gaggauta shawo kan lamarin.
Kakakin rundunar yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da gano abun fashewar, ya ce sun tura dakarun kwance Bam zuwa yankin.
Yace:
"Tuni aka hana mutane zuwa wurin domin kare su daga cutuwa yayin jami'an mu suka dira wurin domin warware abun."
A wani labarin na daban kuma Kwamishina ya yi murabus daga muƙaminsa, ya sayi Fam ɗin takara a PDP
Kwamishinan muhalli da albarkatun karkashin ƙasa na Enugu ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Mista Edeoga, ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin maida hankali kan burinsa na zama gwamna a 2023.
Asali: Legit.ng