Da Duminsa: Yan bindiga sun ƙone Sakatariyar karamar hukuma a jihar Anambra
- Wasu yan bindiga sun kona Sakatariyar karamar hukumar Nnewi South a jihar Anambra, mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa
- Wani shaida ya tabbatar da cewa Mai gadin wurin ne ya mutu, mutane sun shiga yanayin tashin hankali a yankin
- Kakakin yan sanda na jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya hukumarsu ta kara jibge jami'an tsaro a yankin
Anambra - Mutane sun shiga tashin hankali mara misaltuwa ranar Alhamis yayin da yan bindiga suka ƙona Sakatariyar ƙaramar hukumar Nnewi South, jihar Anambra.
Punch ta rahoto cewa zuwa yanzun an tabbatar da mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa yayin mummunan lamarin da safiyar nan.
Duk da ba'a gama tantance yawan mutanen da lamarin ya shafa ba, amma ana zaton wanda ya mutu shi ne mai gadin Sakatariyar.
Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da cewa mutum da ya rasa ransa yayin harin Mai gadin Sakatariyar ne, kamar yadda Premium times ta rahoto.
Rahotanni daga karamar hukumar sun nuna cewa mazaunan suna cikin tsoro da fargaba game da abin da ka iya zuwa ya dawo.
Wane hali ake ciki yanzu?
Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa, abun ya shafi cinna wuta.
A kalamansa, kakakin yan sandan ya ce:
"Ana tsammanin lamari ne da ya shafi tashin wuta, amma har yanzun babu cikakken bayani."
Duk da cewa kakakin 'yan sanda bai faɗi yawan mutanen da lamarin ya shafa ba, ya kara cewa tuni aka ƙara girke jami'an tsaro a yankin kuma an tuntubi hukumar kashe gobara.
A wani labarin kuma Kwamishina ya yi murabus daga mukaminsa, ya siya Fam ɗin takarar gwamna a 2023
Mista Edeoga, ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin maida hankali kan burinsa na zama gwamna a 2023.
Ya gode wa Allah bisa taimakonsa lokacin da yake kan kujera, ya kuma gode wa gwamna da ma'aikan da ya yi aiki tare da su.
Asali: Legit.ng