Ramadana: A fara duban jinjirin wata daga ranar Juma'a, inji kwamitin ganin wata
- Kwamitin ganin wata na kasa ya fitar da sanarwar lokacin da ya kamata musulmi su fara duba watan Ramadana
- Kwamitin ya bayyana cewa, ranar Juma'a mai zuwa ce 29 ga watan Sha'aban, don haka a fara duban watan
- Hakazalika, ya kuma yi karin haske kan yadda za a tura bayanai ga kwamitin na ganin wata na kasa
Kwamitin ganin wata na kasa (NMSC) ya sanar da cewa, lokaci ya yi da musulman Najeriya za su fara duban watan Ramadana a cikin wannan mako.
Wannan na zuwa ne yayin da musulman duniya ke ci gaba da shirye-shiryen fara Azumin Ramadana na shekara-shekara.
Sanarwar da kwamitin ya fitar a makon nan ta shafinsa na Facebook ya bayyana cewa, ranar Juma'a za ta kasance 29 ga watan Sha'aban na kalandar Islama, wanda ka iya zama ranar karshe na watan.
Kwamitin ya bayyana cewa, musulmi su fara sanya ido daga ranar Juma'a domin duba yiwuwar fitowar watan na Ramadana mai falala.
A cewar sanarwar:
"Juma’a mai zuwa 1 ga Afrilu 2022 (G), ita ce 29 ga Sha’aban 1443 (H) don haka itace ranar farko da za a fara neman jinjirin watan Ramadana 1443 (H).
"Lokacin da ake tsammanin ganin wata a Najeriya shine Juma'a, 1 ga Afrilu, 2022 (G), da misalin karfe 07:24 na safe (06:24am GMT). An ba da wasu bayanan fasaha a cikin hotunan da ke hade anan.
Hakazalika, kwamitin ya roki jama'ar musulmi a kasar da su fara duban watan Ramadana a gobe Juma'a kana su sanar da kwamitin idan aka samu bayanin ganinsa ko wasu bayanai masu amfani.
Sanarwar ta yi karin haske kan yadda za a tura bayanai masu amfani game da watan na Ramadana kamar haka:
"A cikin rahoton ku yana da kyau a bayyana cikakken sunan, wuri (birni) da kuma daidai lokacin da aka duba. Ana ba da shawarar, idan zai yiwu, a nemi jinjirin watan a cikin jama'a."
Sakon kungiyar Izala ga Buhari: Bai kamata ka bari ASUU su ci gaba da yajin aiki ba
A wani labarin, Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS), a ranar Lahadi, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su warware sabanin da ke tsakaninsu tare da janye yajin aikin malaman na jami'a.
Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir ne ya yi wannan kiran a wajen rufe taron karawa juna sani na kwanaki 29 na shirin watan Ramadan mai taken: “Shugabanci nagari da tsarin samar da tsaro ga jama’a” da aka gudanar a garin Jos.
Sheikh Jingir ya ce gwamnatin tarayya a nata bangaren ya kamata ta yi duk mai yiwuwa don ganin an warware matsalar da ke tsakaninta da ASUU domin kawo karshen yajin aikin.
Asali: Legit.ng