Da yiwuwan Shugaba Buhari ya halarci wasan kwallon Najeriya da Ghana, Ministan Wasanni

Da yiwuwan Shugaba Buhari ya halarci wasan kwallon Najeriya da Ghana, Ministan Wasanni

  • Yan wasan kwallon Najeriya Super Eagles zasu buga wasa mai muhimmanci ranar Talata a kasar Ghana
  • Saboda muhimmacin wannan wasa, gwamnatin tarayya ta ce ma''aikatan gwamnati su tafi gida da wuri
  • Ministan wasanni ya ce da yiwuwan shugaban kasa dan kasan a hallari wasan da za'a buga a Abuja

Da alamun shugaba Muhammadu Buhari zai halarci wasan kwallon hayewa gasar kwallon duniya na Qatar 2022 da za'a buga tsakanin Najeriya da Ghana.

Ministan wasanni da matasa, Sunday Dare, ya ce da yiwuwan shugaban kasa ya shiga filin kwallo kallon wasa.

Za'a buga wasan yau Talata, 29 ga Maris, a filin kwallon kasa ta Moshood Abiola dake birnin tarayya Abuja.

Ghanasoccernet.com ta ruwaito Sunday Dare da cewa:

"Ina Legas ranar Talata, 22 ga Maris, sai shugaban kasa ya tambayeni shin me ya sa ban tafi Ghana ba."

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

"Bai bani tabbacin zai halarta ba amma akwai yiwuwan ya yi halartar bazata ranar 29"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hira da manema labara
Da yiwuwan Shugaba Buhari ya halarci wasan kwallon Najeriya da Ghana, Ministan Wasanni Hoto: @NGSuperEagles
Asali: Twitter

An bada umirnin rufe ofishohin gwamnati karfe 1 gobe don bada daman kallon wasar Najeriya da Ghana

Gwamnatin tarayya ta bada umurnin rufe dukkan ma'aikatun gwamnati karfe daya ranar Talata don baiwa mutane daman shirya zuwa halartan wasan kwallon Najeriya da Ghana.

Za'a buga wasa kwallon hayewa gasar kofin duniya a Qatar 2022 ranar Talata a filin kwallon Moshood Abiola dake birnin tarayya Abuja.

Ahmed Musa ya bayyana cewa ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya; Super Eagles za su yi iya kokarinsu wajen ganin sun gamsar da ‘yan Najeriya ta hanyar samo tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022, inda ta alkawarta lallasa Ghana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng