Da Duminsa: Ma'aikatan jami'a karkashin SSANU da NASU sun hargitsa jami'ar Legas

Da Duminsa: Ma'aikatan jami'a karkashin SSANU da NASU sun hargitsa jami'ar Legas

Kwamitin hadin gwiwa na manyan ma’aikatan jami’o’i (SSANU) da NASU reshen Jami’an Lagas sun rufe wutar lantarki da hanyar ruwan jami’ar, bayan fara yajin aikin mako biyu.

An fara yajin aikin ne a daren ranar Lahadi, 27 ga watan Maris, inda suka bi sahun kungiyar ASUU wajen gurguntar da harkokin ilimi a jami’ar.

Da Duminsa: Ma'aikatan jami'a karkashin SSANU da NASU sun hargitsa jami'ar Legas
Da Duminsa: Ma'aikatan jami'a karkashin SSANU da NASU sun hargitsa jami'ar Legas | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Rahoton Daily Trust yace, a cewar kungiyoyin, sun yanke shawarar shiga yajin aikin ne biyo bayan halin ko-in-kula da gwamnati ke nunawa bukatunsu.

Da yake jawabi ga mambobin kungiyar a gaban ginin UNILAG, shugaban SSANU, Kwamrad Showunmi Olushola, wanda aka fi sani da Eki 4 Show, ya koka da gazawar gwamnati wajen sake duba albashin su da kuma rashin aiwatar da alawus din karin girma da kin biyan kudaden masu ritaya da sauransu.

Kara karanta wannan

Tinubu @ 70: Buhari ya tura masa sakon taya murna, ya fadi halayen Tinubu na kirki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma yi Allah-Wadai da tsarin biya na IPPIS.

Bayan taron, mambobin kungiyar sun kai mamaya bangaren wutar lantarki na Akoka Electricity Transmission Station don datse lantarki da hanyar ruwa na jami’ar.

Kwamrad Olushola, da rakiyar takwaransa na NASU, Kwamrad Aderibigbe Ayooluwa, ya ce da wannan mataki, babu abun da zai yi aiki a sansanoni yayin da ake sanya ran rufe dukka ofishoshi.

Ya umurci mambobin kungiyoyin da su zauna a gida tsawon lokacin da za a dauka ana yajin aiki, cewa:

“Babu aikin da yake mai muhimmanci a wannan lokacin, ku kauracewa makaranta.”

Shugabannin kungiyar sun kuma umurci dukka masu tsaro da direbobi su bayar da hadin kai a yajin aikin sannan su zauna a gida yayin da kungiyar ta bi ofis-ofis tana korar mambobinsu da suka zo aiki gida.

Sun ce idan mako biyu ya kare ba tare da gwamnati ta yi wani abu ba, za su tafi yajin aikin sai baba ta gani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng