Da Dumi-Dumi: Tsagin hamayya na shirya gaggarumar zanga-zanga kamar EndSARS, FG ta tona Asiri
- Gwamnatin Najeriya ta zargi jam'iyyar hamayya da shirya wata sabuwar zanga-zanga domin ɓata ayyukan Buhari
- Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ce tsagin hamayya na kokarin rusa Najeriya saboda zafin adawa
- A cewarsa, lokacin da suke adawa ba haka suka yi ba, demokaradiyya ta gaji adawa amma mai hankali
Abuja - Gwamnatin tarayya ta zargi tsagin hamayya da kulla-kullan ɓata gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da ɗaukar siyasa da zafi fiye da ƙima.
The Nation ra rahoto cewa FG na ganin tsagin adawa na kulla-kullan ta da wata zanga-zanga kamar ta EndSARS a faɗin ƙasar nan.
Ta kuma yi Alla-Wadai da shirin yan hamayya na yunkurin ayyana babban taron APC na ƙasa a matsayin ya saɓa doka.
Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, wanda ya ankarar da abinda ke shirin faruwa a taron manema labarai a Abuja, ya bukaci bangaren adawa ka da su tada yamutsi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Punch ta rahoto Ministan ya ce:
"Kamar yadda kuka sani, mutanen dake ɗayan bangaren na iyaa bakin kokarinsu su rikita siyasa, su ɓata ɗumbin nasarorin da gwamnatin mu ta samu, kuma su yaɗa ƙarerayi."
"Ga dukkan alamu ba zasu iya hakurin zaben 2023 ba su gwada sa'arsu a zaɓe.Ta ya mutum zai iya bayanin karar da suka kai a ayyana taron mu da ya saɓa doka? Ta ya zakai bayanin barazanar da suke na shirya wata zanga-zangar EndSARS?"
"Ta ya zamu yi bayanin yadda suke yaɗa farfaganga kan abubuwan dake faruwa a ƙasa, ka nuna rashin tsoro a adawa kuma a natse, a baya mune yan adawa kafin mu zo matakin da muke."
Idan kuka lalata kasar, wacce zaku nemi shugabanta?
Alhaji Muhammed, ya ƙara da cewa lokacin da jam'iyyar APC ke tsagin adawa ba su taɓa tunanin rusa Najeriya ba don kawai sun gaza samun mulki.
"Ko sau ɗaya bamu taɓa tunanin kwace mulki ta hanyar hukuncin Kotu ba. Idan ka lalata ƙasar da kake kokarin shugabanta, to wace ƙasa zaka jagoranta kenan?"
"A ƙullin su na baya-bayan nan, sun fara shirya yadda zasu share dukkan nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu."
"Mutanen da suka durƙusad da ƙasa yanzun sun koma suna sukar masu kokarin gyara ɓarna, sun ce sun shirya ceto Najeriya. Waɗan da suka sace sa'ar Najeriya sune kuma suka koma masu ceto."
A wani labarin kuma Ɗan takarar da shugaba Buhari zai goyi bayan ya gaji kujerar shugaban ƙasa a APC zai ba kowa mamaki
Bayan kammala babban taron APC na ƙasa, a halin yanzun hankula zasu koma kan zaben fitar da ɗan takarar da zai gaji Buhari.
Ana tsammanin APC zata shirya zaɓen a cikin shekarar nan, wanda Mambobin Jam'iyya za su zaɓi wanda suke kauna.
Asali: Legit.ng