Dan sanda ya halaka rayuka 2 yayin da ya yi kokarin tserewa daga masu kama shi a Bauchi
- Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta damko wani ɗan sanda, bisa zarginsa da halaka wasu mutane guda biyu
- Ba tare da jinkiri ba, an kama gami da tsare Lukman Madaki, yayin da ake cigaba da bincikar lamarin da ake zarginsa
- Rundunar ta roki mutane da su natsu sannan kada su dauki doka a hannunsu, kafin a sanar da sakamakon binciken bayan kammalarsa
Bauchi - Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta kama wani ɗan sanda mai suna Lukman Madaki, bayan ya halaka mutanen jihar guda biyu.
Kamar yadda takarda da ta fita ranar Juma'a daga Ahmed Wakil, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, lamarin ya auku ne a ranar Alhamis, TheCable ta ruwaito.
An gano yadda aka kai hari ga mazauna yankin, wadanda suke mambobin kwamitin wanzar da tsaro da zaman lafiya tare da wasu jami'an tsaro yayin da suka fita sintiri.
Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya
Ana wannan halin ne, Madaki, wanda yayi kokarin tserewa a lokacin da aka yi kokarin kama shi, ya daɓawa uku daga cikin mambobin wanzar da zaman lafiya makami, inda biyu daga cikinsu suka rasa rayukansu.
"A ranar 24 ga watan Maris, 2022, misalin karfe 10:30 na dare, tawagar sintirin dake karkashin E Division, yayin kai komo a wuraren Rafin Zurfi a Yelwa, ta kama ɗan sanda Lukman Madaki, mai lamba 519342, ɗan shekara 29 na Toro Division wanda ke aiki karkashin ofishin wasanni a Hedkwatar rundunar ƴan sandan jihar," kamar yadda takardar ta bayyana.
"A lokacin da aka yi kokarin kama shi, PC Lukman yayi amfani da sharɓeɓiyar wuka, inda ya daɓa, gami da raunata mambobin kwamitin wanzar da zaman lafiya na tawagar sintirinn: Abdulmalik Muhammad, mai shekaru 22 na Sabon Gida Yelwa; Sadiq mai shekaru 23 na Sabon Gida Yelwa; da Nazifi Muhammad, mai shekaru 19.
"An garzaya da wadanda lamarin ya auku dasu Asibitin Koyarwa na Bauchi don samun kulawan gaggawa, inda likita ya tabbatar da mutuwar Abdulmalik Muhammad da Sadiq, yayin da Nazifi Muhammad ke samun sauki.
"Tuni aka damko wanda ake zargin, gami da tsare shi, yayin da ake cigaba da bincike."
TheCable ta ruwaito cewa, Wakil ya kara da bayyana yadda kwamishinan ƴan sandan Bauchi ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mambobin da suka rasa rayukansu, sannan yayi umarni da tsananta bincikar lamarin.
Sai dai, rundunar ta roki mazauna yankin da su natsu kuma kada su dauki doka a hannunsu, yayin za'a sanar musu da sakamakon bunciken.
Asali: Legit.ng