Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya

Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya

  • Matashi Naziru mai shekaru 25 ya lakadawa kakarsa mugun duka inda ya halakata tare da wurga gawarta cikin wata rijiya
  • Kamar yadda ya sanar da yan sanda bayan an kama shi, ya ce sai da yayi tatul da kwayoyi kafin ya fara aika-aikar da yayi a ranar Alhamis
  • Tuni yan sanda suka cafke shi tare da cire gawar kakar mai shekaru 80 daga rijiya inda aka mika ta asibiti aka tabbatar da mutuwarta

Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Naziru Magaji mai shekaru 25 da laifin kashe tsohuwar kakarsa mai shekaru 80 a duniya, shafin LIB suka ruwaito.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a 25 ga watan Maris, ya ce wanda ake zargin ya nada wa tsohuwar matar duka, wacce ta kasance kakarsa, sannan ya jefa ta cikin wata tsohuwar rijiya mai zurfi.

Kara karanta wannan

Tsakaninmu Ne: Magidanci Ya Faɗa Wa Ƴan Sanda Yayin Da Suke Tuhumar Matarsa Da Yunƙurin Datse Masa Mazakuta

Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya
Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC
“A ranar 24/03/2022 da misalin karfe 1 na dare ne aka samu korafi daga wani mazaunin kauyen Wangara da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano kan cewa, a daidai wannan rana da misalin karfe 12, wani Naziru Magaji dan shekara 25 a duniya ya yi aika-aikar.
“Mazaunin Kununu Yalwa Danziyal da ke karamar hukumar Rimin Gado, jihar Kano, ya lakada wa kakarsa, wata Habiba Abubakar, mai shekaru 80 dukan tsiya, sannan ta jefa gawarta a wata tsohuwar rijiya mai zurfi,” in ji kakakin rundunar yan sandan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da samun rahoton kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umurci tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Isiyaku Mustapha Daura, jami’in ‘yan sanda na yankin Tofa da su garzaya wurin da lamarin ya faru.

LIB sun ruwaito cewa, nan take tawagar ta je isa inda lamarin ya faru, suka dauka gawar daga rijiyar, sannan suka garzaya zuwa babban asibitin Tofa inda aka duba tsohuwar kuma likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

“A binciken farko, wanda ake zargin ya amsa cewa lafiyar kwakwalwarsa daya, ya lakada wa kakarsa ‘yar shekara 80 dukan tsiya, ya jefar da gawarta a cikin rijiya, kuma ya aikata hakan ne bayan ya sha maganin sa maye mai suna exol. Ya kara da cewa ya dade yana dabi'ar shan kwayoyi masu sa maye, don haka mahaifiyarsa ta gargade shi sau da yawa kan cewa ya daina aikata hakan, amma ya ki bin shawarar ta."

An mayar da lamarin zuwa sashin binciken laifuka na rundunar ‘yan sanda, inda daga nan ne za a mika wanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya yi gargadin cewa masu aikata laifuka ba za su samu mafaka a jihar Kano ba.

Ya kara da shawartar su da su tuba ko su bar jihar baki daya. Idan ba haka ba, za a kama su kuma su fuskanci fushin hukuma.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya rafke matar aure da tabarya, ya halakata a gaban yaranta a Kano

Ya mika godiyarsa ga gwamnatin jihar Kano, mutanen jihar, sauran jami’an tsaro, kungiyoyin farar hula (CSOs), da masu ruwa da tsaki kan harkokin ‘yan sanda bisa addu’o’i, karfafa gwiwa, goyon baya da hadin kai.

Ya bukaci mazauna jihar da su yi wa jiha da kasa addu’a tare da kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su, tare da gujewa daukar doka a hannunsu.

CP ya kara da cewa, za a ci gaba da sintiri babu kakkautawa, kai samame na maboyar masu aikata laifuka, a duk fadin jihar, yayin da hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan "Operation Puff Adder" da ke ci gaba da yin la'akari da saurin amsa kiran gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel