Kudin Paris Club: Kotu ta yi watsi da wata kara da jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin Buhari

Kudin Paris Club: Kotu ta yi watsi da wata kara da jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin Buhari

  • Kotun babba birnin tarayya ta yi watsi da karar da manyan lauyoyin jihohin Najeriya suka shigar kan gwamnatin tarayya
  • A baya lauyoyin sun shigar da karar ne kan batun da ya shafi mayar da kudaden Paris Club, inji rahotanni
  • Bayan dogon lokaci, kotun ta bayyana dalilan da ta yi la'akari dasu wajen yin watsi da wannan kara

Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da manyan lauyoyin gwamnatin jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin tarayya.

A cikin karar, jihohin na kalubalantar shirin cire dala miliyan 418 daga asusun tarayya don biyan basussukan da wasu masu ba da shawara na jihohi da kananan hukumomi ke bin su dangane da kudaden Paris Club.

Kotu ta yi watsi da karar mayar da kudin Paris Club
Kudin Paris Club: Kotu ta yi watsi da wata kara da jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin Buhari | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi watsi da karar ne a wani hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a, yana mai cewa manyan lauyoyin ba su kawo isassun shaidun da za su ba su gamsar da kotu ba.

Kara karanta wannan

An kai wa Buhari kukan wasu Gwamnoni 2, an nemi ya ja masu kunne da kyau kafin 2023

Kafar yada labarai ta Channels Tv ta ruwaito cewa, alkalin ya ce babu wata kwakkwarar hujja da ta nuna cewa gwamnonin jihohin 36 sun amince da shigar da karar.

A cewar alkalin, an samar da ofishin babban Lauyan Jiha ne a karkashin sashe na 195 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999, sannan kuma AG na jiha gwamna ne ke nada shi, wanda hakan ya sa AG ya zama wanda ke aiki a karkashin ikon wani gwamna.

Ya ci gaba da cewa jayayyar da masu shigar da kara suka yi na cewa ba bangaren shari’a ba ne, bai kai ga ci ba, domin kungiyar gwamnonin Najeriya da kungiyar kananan hukumomi sun shiga cikin karar.

Kotun ta ci gaba da cewa wadanda suka shigar da karar sun amince da akwai bashin da ake bi, inda suka dage cewa shigar da karar wata dabara ce ta kalubalantar bashin da ake bi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

Mai shari’a Ekwo ya bayyana cewa matakin da masu shigar da karar suka dauka na nuna cin zarafin tsarin shari’a ne, inda daga bisani ya yi watsi da karar saboda rashin cancantarta.

Kudin Paris Club: Kotu ta yi watsi da wata kara da jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin Buhari

A wani labarin, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da manyan lauyoyin gwamnatin jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin tarayya.

A cikin karar, jihohin na kalubalantar shirin cire dala miliyan 418 daga asusun tarayya don biyan basussukan da wasu masu ba da shawara na jihohi da kananan hukumomi ke bin su dangane da kudaden Paris Club.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi watsi da karar ne a wani hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a, yana mai cewa manyan lauyoyin ba su kawo isassun shaidun da za su ba su gamsar da kotu ba.

Kara karanta wannan

Ban Damu Da Tsige Ni Da Kotu Ta Yi Ba Ko Kaɗan, Har Ƙiba Da Kyau Na Ƙara, Gwamna Umahi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.