An Tsinci Gawar Jarumar Fim Ta Najeriya a Ɗakin Otel Sati Ɗaya Bayan Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarta
- Rundunar yan sanda na Jihar Benue ta tabbatar da cewa an tsinci gawar wata Takor Veronica a dakin otel a unguwar Nyinma
- Yan sanda sun ce an tarar da gawarta da tufafi kuma babu alamun rauni a jikinta wadda hakan na nuna akwai yiwuwar ba kashe ta aka yi ba
- Kakakin yan sandan Benue, Cathrene Anene ta ce a halin yanzu an kama mutum uku da ake zargi da hannu a mutuwar amma likitoci za su yi karin haske
Jihar Benue - An tsinci gawar Jaruma Takor Veronica a cikin wani daki na Otel a Jihar Benue, kamar yadda The Nation ta rahoto.
A cewar rahotanni daban-daban, an gano gawar na Veronica ne kimanin sati baya bayan ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta.
Sai ka kawo mahaifinka ko Malam Liman: Kotu ta ba da sharadin beli ga wanda ya kira Ganduje dan rashawa
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An rahoto cewa an tsinci gawarta ne a wani dakin otel a unguwar Nyinma na Makurdi.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene ta tabbatar da afkuwar lamarin.
An kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisar jarumar, Anene
Kakakin yan sandan ta ce an kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a mutuwar jarumar.
"An kawo rahoton mutuwar wata mata a otel amma muna jiran bayani daga likitoci. Ba mu ga alamun rauni a jikinta ba. Don haka gwajin likitoci zai sanar da mu sanadin mutuwarta. Matar da ta mutu tana sanye da tufafi; ba mu ga alamar rauni a jikinta ba.
"An kama mutane uku da ake zargi da hannu a wannan, za su bamu karin bayani. Ba za mu iya cewa kashe ta aka yi ba domin ba mu ga alamar rauni ba," in ji ta.
Abokanta da abokan aiki sun yi ta wallafa sakon ta'aziyya a dandalin sada zumunta.
Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi
A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.
An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.
Yan sandan suna zarginsa da:
"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".
Asali: Legit.ng