Ku sake bamu dama mu mulki kasar nan: Gwamnonin PDP sun roki yan Najeriya

Ku sake bamu dama mu mulki kasar nan: Gwamnonin PDP sun roki yan Najeriya

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun siffanta mulkin Buhari da APC matsayin annoba ga al'ummar Najeriya
  • Gwamnonin 13 da suka halarci taron sun bukaci yan Najeriya su sake baiwa PDP dama ta mulki kasar nan
  • Sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga matsayinsa na Ministan man fetur

Abia - Kungiyar gwamnonin jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta yi Alla-wadai da hauhawar farashin kayayyaki da kuncin rayuwar da jama'a ke fama da shi a kasar.

Sun yi kira ga yan Najeriya su baiwa jam'iyyarsu damar sake mulkar Najeriya don gyara abubuwa.

Gwamnonin sun gana ne a ranar Laraba a jihar Abia, rahoton TheNation.

Gwamnonin PDP
Ku sake bamu dama mu mulki kasar nan: Gwamnonin PDP sun roki yan Najeriya Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Abdullahi Adamu mukayi ittifakin ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC, Gwamna Sule

A jawabin da suka sake a karshen zaman, gwamnonin sun ce jam'iyyarsu shirya take ta kwace mulki daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a 2023.

Gwamnonin sun ce idan PDP ta samu mulki, za tayi mulki na kwarai tare da magance matsalolin kasar.

Sun baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawarar ya sauka daga matsayinsa na Ministan man fetur saboda ya bayyana cewa ya gaza.

Gwamnoni 13 ne suka halarci wannan zama.

Sun hada da Aminu Tambuwal (Sokoto), Ikpeazu (Abia) , Ahmadu Fintiri (Adamawa) and Udom Emmanuel (Akwa Ibom).

Sauran sune Bala Mohammed (Bauchi), Douye Diri (Bayelsa), Samuel Ortom (Benue), Ifeanyi Okowa (Delta) da Godwin Obaseki (Edo).

‘Yan takarar shugaban kasa na PDP sun gana don zaban daya kwakkwara

A ranar Alhamis din da ta gabata ne ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP suka gana a Abuja, domin yanke shawari da ganin an samar da dan takarar daya kwakkwara gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da Abdullahi Adamu, mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wannan na zuwa ne a matsayin ci gaba da gudanar da taron da aka fara a Bauchi.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki da gwamnonin jihohin Sokoto da Bauchi, Aminu Tambuwal da Bala Mohammed sun gana a Abuja kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng