Dalilin rabuwar kan sauran jam'iyyun siyasa: Babu jam'iyyar da ke da uba kamar Buhari, inji Ahmad Lawan
- Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi magana kan ko me ke ya jawo rashin hadin kan sauran jam’iyyun siyasa
- Lawan a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, ya lura da cewa hakan na iya kasancewa saboda basu da uba kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Jigon na APC ya bayyana Buhari a matsayin uba, inda ya kara da cewa shugaban kasa yana tabbatar da an sasanta rashin jituwa kuma kowa ya samu kwanciyar hankali
Sauran jam’iyyun siyasa a Najeriya “watakila” sun samu rabuwar kai ne saboda ba su da uba kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, wannan batu na zuwa ne daga bakin shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan bayan ganawa da shugabannin majalisar dokokin kasar gabanin babban taron gangamin jam’iyyar APC na kasa.
Lawan da yake magana a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, ya bayyana Buhari a matsayin uban da ke iya tabbatar da an sasanta tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar, kuma kan kowa ya kasance a hade.
Shugaban majalisar dattawan ya ci gaba da cewa a jam’iyyar APC akwai uba kuma shugaban kasa da zai iya tabbatar da cewa jam’iyyar ta ci gaba da kasancewa a dunkule, inji rahoton Channels Tv.
Yace.
“To, duk da dai ba na son nuna bangaranci sosai. Amma ba shakka, idan kuna da uba a cikin ahali da kuma uwa, to za ku iya samun kwanciyar hankali.
"Sannan idan kuna da daya ko babu ko daya a cikin ahali, ba za ku yi nasara ba, ahalin nan da iya samun rabuwar kai, kuma abin da wasu jam’iyyun siyasa ke fuskanta ke nan."
Taron gangamin APC: Gobe Juma'a muke shirin sakin sunayen wadanda muka zaba, Ahmad Lawan
A wani labarin, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya bayyana cewa jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun yarda da yin ittifaki kan wadanda za'a zaba sabbin shugabannin jam'iyyar.
A cewarsa, gabanin taron da za'a yi ranar Asabar, zasu saki jerin sunayen wadanda akayi ittifaki kansu gobe Juma'a.
Yace: "Muna sa ran ittifaki kan wadanda zamu zaba matsayin shugabannin jam'iyyar, shirye muke da samar da jerin wadanda za'a zaba."
Asali: Legit.ng