Kada mu kuskura mu bari PDP ta taba karagar mulki da kazantar hannunta, Buhari

Kada mu kuskura mu bari PDP ta taba karagar mulki da kazantar hannunta, Buhari

  • Shugaba Buhari ya ce ba karamin kuskure bane a bari jam'iyyar PDP ta koma bakin mulki a shekarar 2023
  • Shugaban kasan ya gargadi gwamnonin APC su jajirce kuma su hada kawunansu don APC tayi dodar kan mulki
  • Shugaba Buhari ya zanna da gwamnonin jam'iyyar don dinke barakar dake tsakaninsu

Aso Rock, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kada a kuskura a bari jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta koma kan ragamar mulki a shekarar 2023.

Shugaban kasan a ranar Laraba, 23 ga Maris, ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin gwamnonin APC a fadar shugaban kasa kan taron gangamin jam'iyyar, rahoton Punch.

Musamman shugaban kasa ya fadawa gwamnonin cewa su fifita cigabar jam'iyyar APC akan son mulkinsu.

Buhari
Kada mu kuskura mu bari PDP ta taba karagar mulki da kazantar hannunta, Buhari Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

Shugaban kasa yace jam'iyyar ta yi kokari a shekaru bakwai da suka gabata duk da kalubalen da ta fuskanta.

Yace:

"Kamar yadda na fada lokacin da na zannan daku ranar 22 ga Febrairu, manufarmu itace APC ta yi nasarar cin shugaban kasa da kuma jihohi da dama."
"Kada mu kuskura mu bari PDP ta dafa karagar mulki da kazamar hannunta kuma ta mayar damu ruwa."

Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, shugaban kwamitin labaran taron gangamin APC

Gwamnan jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin Midiya na babban taron APC na ƙasa, Abdullahi Sule, ya yi bayanin abin da yasa gwamnoni suka amince da zaɓin Buhari.

Tribune Online ta rahoto gwamnan na cewa Shugaba Buhari na goyon bayan tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya zama shugaban APC na gaba.

A ranar Asabar 26 ga watan Maris, 2022, APC zata gudanar da babban taronta na ƙasa wanda zata zaɓi shugabanninta.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC: Duk wanda Buhari ya zaba a taron gangamin shi za mu marawa baya

Da yake jawabi ga manema labarai game da shirin da kwamitinsa ya yi, Gwamna Sule ya ce masu shakku kan zabin Buhari sun amince ne saboda girmamawan da Buhari ke samu daga masu faɗa a ji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng