Bayan Lallasa Su, An Zaga Gari Da Wasu Matasa 4 Da Aka Kama Dumu-Dumu Suna 'Satar' Kaji a Gidan Gona

Bayan Lallasa Su, An Zaga Gari Da Wasu Matasa 4 Da Aka Kama Dumu-Dumu Suna 'Satar' Kaji a Gidan Gona

  • Jami'an tsaro yan sa kai da ake kira vigilante sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da satar kaji da wasu abubuwa a gidan gona
  • Majiyoyi daga unguwar da abin ya faru sun ce fusatattun matasa sun amshe mutanen daga hannun yan sa kai sun lakada musu duka
  • Wata majiyar ta ce daya daga cikin mutanen yana aiki a gidan gonar, kuma shi ne ya gayyaci tawagarsa domin su sace kayayyakin cikin dare

Jihar Ogun - An kama wasu matasa hudu, kuma fusatattun matasa sun lallasa su kan zarginsu da sata a wani gidan gona da ke Erunwon a karamar hukumar Ijebu North East ta Jihar Ogun.

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa yan sakai na yankin ne suka kama wadanda ake zargin a daren ranar Talata.

Kara karanta wannan

Daukar fansa: Tsageru sun kone rugar makiyaya kurmus a yankin Kudancin Kaduna

Bayan Lallasa Su, An Zaga Gari Da Wasu Matasa 4 Da Aka Kama Dumu-Dumu Suna 'Satar' Kaji a Gidan Gona.
An kama wasu matasa hudu kan zarginsu da satar kaji a gidan gona. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An rahoto cewa wadanda ake zargin sun tafka sata a gidan gonar, inda suka sace fiye da kaji 100 da buhunan abincin kaji da wasu kayayyaki.

Majiyoyi daga Erunwo sun tabbatar da kama mutanen hudu

Majiyoyi sun ce an kama su ne dumu-dumu a yayin da suke sata a gidan gonar a cikin dare.

Daya daga cikin wadanda ake zargin da aka ce ma'aikaci ne a gidan gonar ne ya gayyaci 'tawagarsa' domin su taho su yi satar.

Majiyar ta ce wani mazaunin yankin ne ya sanar da yan sa-kai din kuma suka kama su, amma fusatattun matasa suka amshe su, sun tube musu tufafi suka zaga da su gari.

Wani daga cikin hotunan da suka bazu a dandalin sada zumunta da Daily Trust ta samu ya nuna wanda ake zargin ba tufafi an kuma daure kafafunsu yayin da kowannensu ke rike da kaza, a matsayin hujja a kansu.

Kara karanta wannan

Abun mamaki: Yadda nakasassun guragu suka cika wandunansa da iska wurin gujewa jami'an tsaro

Daga karshe an mika wadanda ake zargin hannun yan sanda

An kuma gano cewa daga bisani an mika su hannun rundunar yan sanda na Atan, hedkwatar karamar hukumar Ijebu North East.

Da wakilin majiyar Legit.ng ya tuntubi kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce yana kokarin ji ta bakin DPO mai kula da yankin Atan.

Kaduna: Lauya Ya Yi Ƙarar Wani Mutum a Kotun Shari'a Saboda Ƙin Biyansa N100,000 Kuɗin Aikinsa

A wani labarin, wata kamfanin lauyoyi a Kaduna mai suna Moonlight Attorneys, a ranar Litinin, ta yi karar wani Yusha'u Abdullahi a kotun shari'a saboda kin biyan kudin N100,000 kudin aikin da suka masa.

Lauyan wanda ya shigar da karar, Atiku Abdulra'uf, ya bayyana cewa wanda aka yi karar ya nemi wanda ya shigar da karar ya yi masa aiki, kuma suka amince zai biya adadin a matsayin kudin aiki, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

An tashi baktatan a makaranta bisa tsoron harin 'yan bindiga a jihar Imo

Ya yi bayanin cewa bayan an kammala aikin, wanda aka yi karar ya ki biyan kudin duk da yarjejeniya da suka yi, hakan yasa wanda ya shigar da karar ya taho kotu don a bi masa hakkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164