Da Duminsa: Yan bindiga sun sako mutum 75 da suka sace a harin jihar Zamfara
- Yan ta'adda sun amince sun sako mutum 75 da suka yi garkuwa da su a kauyen Yar Katsina, karamar hukumar Bungudu a Zamfara
- Wani mazaunin ƙauyen ya bayyana cewa yan bindigan sun rike wata yarinya yar shekara shida saboda ɗayansu ya maida ta ɗiyarsa
- Maharan sun sace mutanen ne a hare-hare guda biyu da suka kai yankin cikin watanni biyu da suka gabata
Zamfara - Yan bindiga sun sako mutum 75 da suka yi garkuwa da su a ƙauyen Yar Katsina dake ƙarƙashin masarautar Waje a ƙaramar hukumar Bungudu, jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
Mutanen da suka kubuta sun shiga hannun yan ta'addan ne a manyan hare-hare biyu da suka kai ƙauyen su cikin watanni biyu da suka gabata.
Da farko, yan bindigan sun yi awon gaba da mutane 61, bayan kwanaki 36 kuma suka ƙara yin garkuwa da wasu mutum 15.
Wani mazaunin ƙauyen, Sadiq Sani, ya bayyana cewa yan ta'ddan sun rike wata mace ɗaya yar shekara 6 a duniya.
Sani ya ce:
"Yan bindigan sun rike wata ƙaramar yarinya yar shekara shida mai suna Ummi kuma sun aike wa iyayenta sakon cewa zasu rike ta kamar yarsu saboda suna sonta."
"Iyayen Ummi ba su cikin mutanen da aka yi garkuwa da su. Ɗaya daga cikin yan ta'addan ya ce bai taɓa haihuwa ba, don haka zai rike ta a matsayin ɗiyarsa. Ta zama yarsa don ya yi alƙawarin kula da ita."
Shin yan uwa sun biya kuɗin fansa ne kafin sakin mutanen?
Karshen Mako: Yadda yan bindiga suka ɓarnata rayuka 62, sace wasu 62, suka kona gida 70 a Kaduna da Zamfara
Mutumin ya ƙara da cewa sai da mazauna ƙauyen suka tattara miliyan N4m a matsayin fansa kafin yan bindigan suka sako yan uwansu.
"Tuni aka haɗa kowa da iyalansa. Sai dai yan ta'addan sun kafa sharaɗin cewa wajibi Yan Bijilanti su daina amfani da makamai."
Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, bai samu ba bare aji ta bakin hukumarsu kan cigaban.
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa matsalar tsaro ta kori mazauna 700,000 daga gidajen su a faɗin jihar
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ma’aikatar bada agaji ta kafa cibiyoyi takwas domin kula da wadanda su ke sansanin gudun hijira a garuruwan jihar.
Kwamishinan yada labarai na Zamfara, Ibrahim Magaji Dosara ya shaidawa manema labarai a Kaduna cewa gwamnati na dawainiya da masu gudun hijira kusan 700,000.
Asali: Legit.ng