Dan ta'adda ya gudu daga hannun hukuma yayinda aka kaishi kotu

Dan ta'adda ya gudu daga hannun hukuma yayinda aka kaishi kotu

  • Wani matashi da ke gurfana a kotu kan laifin fashi da makami ya sullube daga hannun jami'an tsaro
  • Etiene Akpan ya arce daga hannun yan sanda yayinda aka gurfanar da shi a kotu
  • Kakakin hukumar yan sanda SP Odiko yace ana nemansa ruwa a jallo yanzu

Akwa Ibom - Wani mutumi da ake yiwa zargin ta'addanci ya gudu daga hannun hukuma a jihar Akwa Ibom, hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Akwa Ibom, Odiko MacDon, a jawabin da ya saki ranar Talata, ya bayyana cewa mutumin mai suna Etiene Malachy Akpan, ya gudu daga kotu ne lokacin da aka je gurfanar da shi.

Dan ta'adda ya gudu daga hannun hukuma yayinda aka kaishi kotu
Dan ta'adda ya gudu daga hannun hukuma yayinda aka kaishi kotu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Caccakar Ganduje: 'Yan sandan Kano na neman Bashir Gentile ruwa a jallo kan sukar Ganduje

Kaakin yace an gurfanar da Akpan kan laifin kisan kai, garkuwa da mutane da fashi da makami, rahoton PremiumTimes.

Ya kara da cewa mutumin dan shekaru 34 ne kuma dan asalin Atan Midim a karamar hukumar Abak ta jihar.

Yana da tsayin 1.6m kuma baki ne, cewarsa.

Yace:

"Yan sanda na nemansa bisa alakarsa da fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan ka, da ta'addanci a jihar.'"
"An gurfanar da shi kan wadannan laifuka kuma ya gudu a harabar kotu lokacin da aka je cigaba da shari'arsa."

SP Odiko yace ana nemansa ruwa a jallo.

Ya yi kira ga jama'ar gari su tuntubi hukuma idan suka ga wannan matashi.

Caccakar Ganduje: 'Yan sandan Kano na neman Bashir Gentile ruwa a jallo kan sukar Ganduje

A wani labarin daban, 'yan sanda a Kano suna shirin kama shahararren mai sharhi a kan harkokin siyasa, Bashir Gentile, kan sukar gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje a shirin radiyo, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Tankan Fetur Ta Yi Taho Mu Gamu Da Trela, An Rasa Rai

Mista Gentile ya kasance hadimin tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, sannan kuma hadimi ne ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

A baya-bayan nan, masu sukar gwamnan da dama sun fuskanci hukunci, tsoratarwa daga yan sanda tare da gurfanar da su a gaban wasu alkalan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng