Abun mamaki: Yadda nakasassun guragu suka cika wandunansa da iska wurin gujewa jami'an tsaro

Abun mamaki: Yadda nakasassun guragu suka cika wandunansa da iska wurin gujewa jami'an tsaro

  • Wani lamari mai kama da wasan kwaikwayo ya faru a kasar Kenya yayin da jamian tsaro suka fita atisayen hana barace-barace a tituna
  • Wasu kanannadaddun guragu da ke kan keke ba su ya iya tafiya, sun cika wandunansa da iska inda suka tserewa jamian tsaro wurin ceton kansu
  • A yayin da aka zanta da mabaratan, sun bayyana cewa bara ce hanya mafi sauki da suke samun kudi har suke mallakar kadarori da gidaje

Lamarin tamkar wasan kwaikwayo da kaduwa tare da rashin imani sun cika garin Thika na kasar Kenya a yayin wani atisaye na kalubalantar barace-barace a kan tituna.

An kama wasu marabatan amma wasu da suka kai 38 daga cikinsu suka gudu domin ceton rayukansu kafin 'yan sanda su kama su.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan sanda sun karbe majalisar Cross River bayan tsige yan majalisa 20

‘Yan sandan sun kai samame garin a ranar Asabar din da ta gabata inda suka damke mabaratan da suka addabi al’ummar garin, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Abun mamaki: Yadda kanannadadden gurgu ya cika wandonsa da iska wurin gujewa jami'an tsaro
Abun mamaki: Yadda kanannadadden gurgu ya cika wandonsa da iska wurin gujewa jami'an tsaro. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

A yayin atisayen, mabaratan kan tituna sun nuna yadda suke karyar raunuka da nakasu wajen neman kudi a hannun jama'a.

Wasu da aka san suna rarrafe a kan tituna ko kuma suna kan keken guragu na dindindin sun fi ‘yan sanda gudu da sauri kuma suka bace a kan tituna.

Shafin Linda Ikeji ta ruwaito cewa, daya daga cikinsu wata mace ce, wacce kafin a kai farmakin tana rarrafe a kasa amma bayan biyo ta da aka yi sai ta mike da kafafunta tana tafiya da kanta.

Atisayen da ‘yan sanda da na kananan yara suka yi ya samo asali ne sakamakon yawaitar barace-barace da aka yi a garin Thika da aka kai hari kan manyan hanyoyi, manyan kantuna da manyan tituna.

Kara karanta wannan

Daukar fansa: Fusatattun matasa sun far wa matafiya a wani yankin Kaduna

Abin mamaki, mabaratan da aka ce yawancinsu sun fito ne daga makwabciyar kasar Tanzaniya kuma ana daukar su daga Nairobi, sun bayyana cewa suna samun sama da Ksh 150,000 a cikin watan da ba a samu alheri ba.

Sun ce ta hanyar barace-barace ya zuwa yanzu sun samu jari mai tarin yawa a harkokin kasuwanci da kuma sun mallaki gidaje.

Wani matashi dan kasar Tanzaniya, Geoffrey Sawunda, ya shaidawa gidan talabijin na Kameme cewa yana aiki da ubangidansa mata kuma suna samun kusan KSh 4,500 a kowanne rana.

"Muna neman kudi a nan Thika, sannan zuwa Kayole da sauran wurare, a rana daya za mu iya samun kusan KSh 4,500 don haka muna raba wannan kudin ga uwardakina mai suna Mama Mwaru," in ji shi, ya kara da cewa tana zaune a Kariobangi.

Stephen Kitavi, dan shekara 21 mai haihuwa daya, ya tashi daga kasuwar Donyo Sabuk kuma yana yawan zuwa Thika. Ya ce yana samun sama da Ksh70,000 a wata, wanda ya isa ya tallafa wa danginsa da saka hannun jari kadan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun sheke dagacin kauye da wasu mutum 19

“Na yi hatsari shekaru da suka wuce amma na warke. Ina yin kamar ni nakasasshe ne don samun taimako a tituna. Tare da kayana na tafiya, na isa garin Thika da misalin karfe 6:00 na safe kuma saboda an san ni a kusa da su, mutane ba sa jin wahala wajen taimaka mani,” a cewar shi.

Ban da wasu na nufin mutanen da suke yi masu mugun baki idan sun nemi taimako, sun ce bara hanya ce mai sauki ta samun kudi.

"Karamcin da 'yan kasar Kenya ke yi bai misaltu ba. Da akwati kawai da keken guragu, kuna karyar nakasa kuma za ku iya jan hankalinsu. Ina gaya muku da yamma, ba za ku rasa Ksh2,000 ko fiye ba," Evelyne Maria, wata mabaraciya tace.

Jami’ar kula da kananan yara ta yankin Thika Lina Mwangi ta ce akasarin wadanda aka kama na amfani da yara ne don nuna tausayi yayin da suke bara. Ta yi gargadin cewa ba za su bari a yi amfani da yara a matsayin barace-barace a kan titi ba. Ta ce daga cikin mutane 38 da aka kama, biyu ne kawai 'yan kasar Kenya.

Kara karanta wannan

Kano: Yadda Alkali Aminu Gabari ya karbi cin hancin zunzurutun kudi daga mai korafi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng