Idan yan Najeriya suka zabeni, yan kasa da shekaru 35 zan nada Ministoci: Saraki
- Bukola Saraki ya bayyana cewa ya yi imani matasa ne zasu ciyar da kasar nan gaba a halin da ake ciki
- Tsohon gwamnan ya yi alkawarin cewa dukkan ministocin da zai nada matasa ne yan kasa da shekaru 35
- Bukola ya yanki tikitin takarar kujeran shugabancin kasar nan a zaben da zai gudana a 2023 karkashin jam'iyyar PDP
Tsohon shugaban majalisar dattawan tarayya, Bukola Saraki, ya lashi takobin nada matasa masu shekaru kasa da 35 idan yan Najeriya suka zabeshi matsayin shugaban kasa a 2023.
Saraki wanda ya mulki jihar Kwara tsakanin 2003 da 2011 ya yi wannan alkawari ne ranar Talata, 22 ga watan Maris a shafinsa na Tuwita, Saraki yace:
"Zan yi aiki fiye da yadda nayi niyya. Ina alkawarin cika burikan dukkan matasanmu."
"Ina mai alkawarin cewa idan na zama shugaban kasa a ranar 29 ga Maris, 2023, dukkan Ministoci na zasu kasance kwararrun matasa yan kasa da shekaru 35."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya caccaki jam'iyyar APC mai mulki, inda yace jam’iyya ce mai cike da yaudara da mayaudara.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, ya bayyana hakan ne a Bauchi, a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, lokacin da kwamitin yakin neman zabensa ya ziyarci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP domin neman shawari a sakateriyar jam’iyyar a Bauchi.
Saraki wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa a 2023, Farfesa Tyorwuese Hagher, ya ce APC ta kasa cika alkawuran da ta dauka wa ‘yan Najeriya a yakin neman zaben 2015.
Asali: Legit.ng