Za'a bude katafaren Masallacin da hedkwatar Izalah ta gina da fatun Layya a Abuja
- Kungiyar Izalah ta kammala ginin sabon Masallaci a unguwar Utako dake birnin tarayya Abuja
- Kungiyar ta bayyana cewa za'a bude wannan Masallaci ranar Juma'a mai zuwa don fara Sallah ciki
- Izalah ta ce an gina Masallacin ne da kudin fatun layyan da ake karba hannun jama'a lokacin Sallar Eidul Adha
Abuja - Kungiyar da'awa ta addinin Musulunci, Jama'atu Izalatul Bid'a Wa iqaamatus Sunna JIBWIS za ta bude sabon Masallacin da ta gina a birnin tarayya Abuja ranar Juma'a.
Jibwis a jawabin da ta saki ranar Talata ta bayyana cewa an gina ne da kudaden fatun layya da mutane ke badawa fisabilillah.
Izalah ta bayyana hotunan Masalaccin dake unguwar Utako, kwaryar garin Abuja.
Jawabin yace:
"Wannan shine Sabon masallacin da Izala ta gina da kudaden fatun layyan da kuka bada sadaka a unguwar Utako dake tsakiyar birnin Abuja a Naijeriya.
Masallacin angina shi karkashin jagorancin Shugaban IZALA Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, kuma an masa aiki na musamman wanda za’a jima ana morar sa.
Kuma Ranar Juma’an nan dake tafe za’a bude masallacin domin fara sallah da sauran ayyuka na ibada a ciki insha Allah.
Jin-jina na musamman ga shugaba Sheikh Bala Lau, da sauran shugabanni masu Rufa masa baya. Allah ya saka wa kowa da alheri. Amin."
Kalli hotunan Masallacin:
Kungiyar Izala ta rabawa yan gudun Hijra da matsalar tsaro ta shafa a Neja kayayayyki
A wani labarin, kungiyar JIBWIS ta kai dauki ga al'ummar jihar Neja da rikicin rashin tsaro ya kora daga muhallansu.
Kayan da aka raba sun hada da hatsi, tufafi da kayan shayi.
Izalah a jawabin da ta saki ta bayyana cewa shugabanninta na reshen Neja sun raba wadannan kayan abinci ne ga yan gudun Hijra daga kananan hukumomin jihar 13.
Kungiyar tace "ta bada wannan tallafi ne ga yan gudun hijira dan rage masu radadin da suke fama dashi na rayuwa sakamakon fitin tinun yan ta'adda da ya raba su da garuruwan su."
Asali: Legit.ng