Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira jihar Legas kaddamar da ayyuka
- Bayan makonni biyu a Landan, Shugaba Buhari zai yi tafiyarsa na farko kaddamar da ayyuka
- An kammala ginin sashen kasa da kasa na tashar jirgin saman Murtala Muhammad dake jihar Legas
- Shugaban kasan hakazalika zai duba wasu ayyuka dake gudana ba'a karasa ba
Legas - Shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Legas domin yawun ganin ido da kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin tarayya da Dangote suka yi.
Jirginsa ya dira tashar jirgin Murtala Muhammad misalin karfe 10 na safe.
Shugaban kasan ya samu tarba daga wajen gwamnan Babajide Sanwo-Olu da wasu mambobin gwamnatinsa.
Daga baya ya hau jirgi mai saukar ungulu zuwa unguwar Lekki don kaddamar da masana'antar kada takin Dangote.
Hakazalika Shugaban kasan zai duba ginin matatar man Dangote da ake kan ginawa da kuma tashar ruwan Lekki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP
A wani labari, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya caccaki jam'iyyar APC mai mulki, inda yace jam’iyya ce mai cike da yaudara da mayaudara.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, ya bayyana hakan ne a Bauchi, a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, lokacin da kwamitin yakin neman zabensa ya ziyarci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP domin neman shawari a sakateriyar jam’iyyar a Bauchi.
Saraki wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa a 2023, Farfesa Tyorwuese Hagher, ya ce APC ta kasa cika alkawuran da ta dauka wa ‘yan Najeriya a yakin neman zaben 2015.
Asali: Legit.ng