Jerin sunayen yan majalisar dokoki 20 da kotu ta kora kan sauya sheka daga PDP zuwa APC
Birnin tarayya Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta sallami wasu mambobin majalisar dokokin jihar Cross River su 20 a ranar Litinin, 21 ga watan Maris.
Kotu ta kwace kujerun su ne saboda sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki.
Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Taiwo Taiwo ya yanke, ya riki cewa ya zama dole yan majalisar su sauka daga kujerunsu kasancewar sun yi watsi da jam’iyyar da ta dauki nauyin kawo su kan mulki.
Hukuncin ya biyo bayan wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/975/2021, da PDP ta shigar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga jerin sunayen yan majalisan Cross River 20 da kotu ta fitittika:
1. Michael Ataba
2. Legor Idagbor
3. Eteng Jonnah William
4. Joseph A. Basset
5. Odey Peter Agbe
6. Okon E. Ephraim
7. Regina E. Anyone
8. Matthew S. Olory
9. Ekpo Ekpo Bassey
10.Ogbor Ogbor Udop
11. Ekpe Charles Okon
12. Hillary Ekpang Bisong
13. Francis B. Asuqo
14. Elvert Ayambem
15. Davis Etta
16. Sunday U. Achunekan
17. Cynthia Nkasi
18. Edward Ajang
19. Chris Nja-Mbu Ogar
20. Maria Akawaji
Yan sanda sun karbe majalisar Cross River bayan tsige yan majalisa 20
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun karbe dukka hanyoyin da ke sada mutum ga harabar majalisar dokokin jihar Cross River.
Sun mamaye wuraren ne tun da misalin karfe 6:00 na asubahi kamar yadda shaidu suka bayyana.
Sashin yan sandan da ke kasa sun hada da na yaki da garkuwa da mutane, masu yaki da kungiyar asiri da kuma jami’an yan sanda na yau da kullum, dukkansu dauke da makamai.
The Sun ta kuma rahoto cewa an hangi wasun su na cikin harabar majalisar dokokin.
Asali: Legit.ng