Da dumi-dumi: EFCC ta gano jami'in da ya yada bidiyon gwamna Obiano, za ta ladabtar dashi

Da dumi-dumi: EFCC ta gano jami'in da ya yada bidiyon gwamna Obiano, za ta ladabtar dashi

  • Hukumar EFCC ta nesanta kanta daga wani bidiyo da ke ta yawo na tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano wanda ke tsare a hannunta
  • EFCC ta ce ta gano jami'inta da ya nada da yada bidiyon tsohon gwamnan
  • Hukumar yaki da rashawar ta kuma tabbatar da cewar a yanzu haka yana fuskantar hukunci na ladabtarwa kan haka

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta bayyana cewa ta gano jami’inta da ke da alhakin nada da fitar da bidiyon tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano wanda ke tsare a hannunta.

EFCC ta kuma bayyana cewa za ta dauki matakin ladabtar da jami’in bayan ta same shi da hannu dumu-dumu a aikata laifin.

A ranar Lahadi, 21 ga watan Maris ne wani bidiyo na Obiano sanye da gajeren wando da rigar shirt a tsare a hukumar EFCC ya dunga yawo a shafukan soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

Da dumi-dumi: EFCC ta gano jami'in da ya yada bidiyon gwamna Obiano, za ta ladabtar dashi
EFCC ta gano jami'in da ya yada bidiyon gwamna Obiano, za ta ladabtar dashi Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Batun bankado jami’in da ya aikata hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Facebook, tana mai cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An janyo hankalin hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa, EFCC, zuwa ga wani bidiyo da ke yawo wanda ke nuna tsohon Gwamnan jihar Anambra, Cif Willie Obiano a tsare karkashin kulawar hukumar.
"Hukumar na son nesanta kanta daga wannan bidiyo wanda ya saba ka’idar aiki na EFCC.
"Wani bincike mai zurfi da aka bayar da umunin yi bayan gano bidiyon ya nuna jami’in da ke da alhakin aikata wannan mugun aiki kuma a yanzu haka yana fuskantar hukuncin ladabtarwa da ya dace."

Shugaban EFCC, Bawa, ya yi martani kan kamen tsohon gwamna, zargin cin zarafinsa a siyasance

A gefe guda, mun ji cewa hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC), ta ce kamen Willie Obiano, tsohon gwamnan jihar Anambra tare da yi masa tambayoyi ba siyasa ba ne.

Kara karanta wannan

Sunayen Gwamnoni 33 a Najeriya da hukumar EFCC ta kama bayan tube musu rigar kariya

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata a yayin da yake gabatar da amsar tambayoyi daga manema labarai a babban taron shekara-shekara na cibiyar yaki da cin hanci da rashawa a yammacin Afirka (NACIWA) karo na 5.

Bawa ya kara da cewa, hukumar ta bayar da belin Mista Obiano amma har yanzu tsohon gwamnan bai cika sharuddan belin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng