Ku saki Obiano komu mamaye Hedkwatarku tsirara, Matan Anambra sun ja kunnen EFCC
- Ƙungiyar matan jihar Anambra ta yi barazanar cewa ƴaƴanta zasu fito har Hedkwatar EFFC zanga-zanga kuma tsirara
- Shugabar matan ta ce zasu ɗauki wannan matakin ne matukar EFCC ba ta sako tsohon gwamna Obiano ba
- Ta yi Allah wadai da Bidiyon Obiano dake yawo a kafafen sada zumunta wanda ya nuna shi zaune yana shan ruwa a Ofishin EFCC
Abuja - Wata ƙungiyar mata a jihar Anambra, ta yi barazanar mamaye hedkwatar hukumar EFCC dake Abuja ba tare da kaya a jikin su ba.
Punch ta rahoto cewa ƙungiyar mai suna, 'Anambra-North Women Empowerment Movement' ta yi barazanar ne matukar hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙi sako tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano.
Ƙungiyar ta yi Allah wadai da wani Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka ga Obiano na shan ruwa a Ofishin EFCC da yake tsare.
A wata sanarwa da kungiyar ta raba wa yan jarida a Awka, ranar Litinin, shugabar ƙungiyar Uju Ifunanya Edochie, ta zargi EFCC da nuna tozarci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Ƙungiyar mu na kakkausan gargaɗi ga EFCC bisa tozarci da halin rashin ɗa'a wajen tafiyar da lamarin Obiano. Mu mata da babbar murya muna Allah wadai da Bidiyon Obiano dake yawo a Intanet."
"Tsohon gwamnan na ɗaya cikin gwamnonin da suka fi aiki a Najeriya, domin ya yi abin azo a gani a bangaren Ilimi, Lafiya, Noma, ciniki da kasuwanci, tsaro, samar da aikin yi da tattalin arzikin jiha."
"Jihar Anambra ba ta cikin sahun farko na jihohin dake kan gaba wajen yawan Talakawa, rashin aikin yi ya ragu a zamaninsa saboda manyan ayyukan da ya zuba wa al'umma."
Zamu fito tsirara - Inji kungiyar matan Anambra
Edochie ta ƙara da jaddada cewa, "Ofishin EFCC kan shi bai tsira ba, matuƙar zasu tozarta tsohon gwamnan, kuma su ɗauki Bidiyonsa a wurin da ya kamata su tsare shi har a sake shi a Soshiyal Midiya."
Haka nan kuma kungiyar ta yi barazanar, "gudanar da zanga-zanga har babban Ofishin EFCC dake Abuja kuma tsirara matuƙar hukumar ba ta saki Obiano cikin gaggawa ba."
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta yi babban rashi a Kwara, Ɗan a mutun Bukola Saraki ya sauya sheka zuwa APC
Jam'iyyar PDP ta ɗauki matakin dakatarwa kan tsohon kwamishinan ilimi kuma ɗan amutun Saraki, Injiniya Musa Yeketi.
Sai dai bayan faruwar haka, Misata Yeketi, ya bayyana ficewarsa daga PDP, tare da komawa jam'iyyar APC mai mulki a jihar.
Asali: Legit.ng