Shugaban EFCC, Bawa, ya yi martani kan kamen tsohon gwamna, zargin cin zarafinsa a siyasance
- Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya sanar da cewa kamen tsohon gwamna Willie Obiano ba shi da alaka da siyasa
- Ya bayyana hakana ne yayin amsa tambayoyin manema labarai a yayin taro kashi na 5 na NACIWA da aka yi
- Bawa ya bayyana cewa sun bayar da belin tsohon gwamna Obiano amma har yanzu bai cike sharuddan belin ba
Hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC), ta ce kamen Willie Obiano, tsohon gwamnan jihar Anambra tare da yi masa tambayoyi ba siyasa ba ne, Premium Times ta ruwaito
Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata a yayin da yake gabatar da amsar tambayoyi daga manema labarai a babban taron shekara-shekara na cibiyar yaki da cin hanci da rashawa a yammacin Afirka (NACIWA) karo na 5.
Bawa ya kara da cewa, hukumar ta bayar da belin Mista Obiano amma har yanzu tsohon gwamnan bai cika sharuddan belin ba.
“Babu wani abu na siyasa game da tsare tsohon gwamnan jihar Anambra, Wille Obiano. An bayar da belinsa. Amma muna jiran lokacin da zai cika sharuddan belinsa,” a cewar Bawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kama tsohon gwamna Obiano ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da misalin karfe 8:30 na daren ranar Alhamis.
Wasu majiyoyi a hukumar da suka nemi a sakaya sunansu saboda ba su da izinin yin magana da manema labarai a kan lamarin, sun ce an kama Obiano ne a lokacin da yake shirin shiga jirgin da zai je birnin Houston na jihar Texas ta Amurka.
A ranar Juma’a, an mayar da shi Abuja domin ci gaba da yi masa tambayoyi daga ofishin hukumar EFCC na shiyyar Legas, inda aka fara tsare shi, Premium Times ta ruwaito
Da safiyar ranar Litinin ne tsohon Obiano ya kwana na hudu a hannun hukumar EFCC.
Bidiyon tsohon gwamna yana shan ruwa cike da damuwa a ofishin EFCC
A wani labari na daban, mai rajin kare hakkin da Adam, Deji Adeyanju, ya wallafa wani bidiyo na tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya na shan ruwan gora yayin da ya ke ofishin hukumar yaki da rashawa tare hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Idan za a tuna, an yi ram da tsohon gwamnan jihar Anambran a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas yayin da yake kokarin tafiya Houston, Ingila.
Wannan kamen ya zo ne sa'o'i kadan bayan gwamnan kudu maso gabas din ya mika mulki ga sabon gwamna Charles Soludo.
Asali: Legit.ng