Shugabar APC ta mutu a wajen musayar wuta tsakanin ‘Yan bindiga da ‘Yan banga
- Kwanakin baya ne ‘Yan bindiga suka yi garkuwa da wasu shugabannin jam’iyyar APC a Kwara
- Daga ciki har da wasu jagorori na mata na APC a wasu mazabu wanda yanzu haka ta rasa ranta
- Olomi Sunday ta cika ne a yayin da ‘Yan banga suke musayar wuta da wadannan miyagun mutane
Kwara - Wata shugabar mata a jam’iyyar APC a yankin Koro, karamar hukumar Ekiti, jihar Kwara ta gamu da ajalinta a hannun ‘yan bindigan da suka sace ta.
Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris 2022 cewa Olomi Sunday ta mutu ne yayin da wasu ‘yan sa-kai ke kokarin kubutar da ita a jiya.
Wannan Baiwar Allah ta na cikin shugabannin mata na jam’iyyar APC uku da aka yi garkuwa da su a hanyarsu ta dawowa daga wajen wani taron jam’iyya.
Jaridar ta ce an gudanar da taron rantsar da shugabannin jam’iyyar APC mai mulki da aka zaba ne a gidan gwamnatin jihar Kwara a wancan makon da ya wuce.
Baya ga wadannan mata, an kuma dauke wasu maza uku a wata mota da ta fito daga jihar Ekiti. ‘Yan bindigan sun bukaci a biya N20m a matsayin kudin fansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alasi da Oloke sun sha
Sauran matan da aka dauke su ne Reachel Alasi (shugabar mata ta mazabar Obbo Ayegunle) da takwararta, Yemisi Oloke Oni (shugabar mata ta mazabar Eruku).
Ita Olomi Sunday ce ta rasa ran ta a yayin da ake barin wuta tsakanin wadannan miyagu da suka dauke su da kuma ‘yan bangan da su ke kokarin kubutar da su.
Kamar yadda mu ka samu rahoto daga wata majiya, an tara wannan kudi har N20m za a biya ‘yan bindigan, amma ‘yan banga na sa-kai suka ce za su iya ceto su.
Wannan ya jawo aka yi ta zuba barin wuta a ranar Lahadi, a haka ne aka rasa Olomi Sunday.
Wasu sun samu rauni
Sauran duk sun kubuta, a cikin mazan da aka dauke akwai wadanda suka samu rauni a harin. Sai da na su bai yi muni sosai ba, mutum guda ne ke jinya a asibiti.
Wani ‘dan siyasa a jihar Kwara, Hon Ganiyu Gabriel Afolarin ya tabbatarwa manema labarai cewa shugabar mata ta APC ta mazabar Eruku ta cika a ranar Lahadi.
Saliu Atawodi v EFCC
Ku na sa labari cewa tun 2015 ake zargin VM Saliu Atawodi (rtd) da hannu a badakalar N600m na kudin makamai, sai yanzu aka kammala shari’a a kotun Abuja.
A makon jiya Alkalin babban kotun tarayya, Emeka Chikere ya amince EFCC ta karbe dukiyar tsohon sojan da mai dakinsa, a maida asusun gwamnatin kasa.
Asali: Legit.ng