Jiragen Super Tucano sun yi lugude a maboyar ISWAP, Sani Shuwaram ya shura lahira, an nada sabon shugaba
- Sani Shuwaram, shugaban kungiyar taaddanci ta ISWAP ya sheka lahira sakamakon ruwan wutar da Super Tucanos suka yi a maboyarsu ta Marte
- Majiyar sirri ta sanar da cewa jiragen sun saki ruwan bama-bamai kan miyagun a sansaninsu da ke Tumbun a yankin tafkin Chadi
- Sai da majiyar da ta bukaci a adana sunanta ta tabbatar da cewa an rantsar da sabon shugaba mai suna Mallam Bako Gorgore
Shugaban muguwar kungiyar ISWAP, Sani Shuwaram ya shura lahira sakamakon luguden da jiragen sojin sama na Super Tucano suka yi a yankin Marte da ke jihar Borno.
Rahoton ya ce jiragen Super Tucanos da wasu jiragen sama na sojin saman Najeriya, sun saki ruwan bama-bamai babu kakkautawa a cikin Gatari da sauran sansanonin Shuwaram suke.
Shuwaram ya shura lahira ne saboda harbin bindiga da ya same shi a lokacin da jiragen yakin sojoji suka kai samame sansanin ISWAP da ke Sabon Tumbuns na tafkin Chadi.
Hakazalika, wata majiyar sirri da ta tsaro a yankin Arewa maso Gabas ta tabbatar da labarin kisan Shuwaram wanda ya shaida wa PRNigeria amma ya bukaci a sakaya sunansa.
“Shuwaram yana daga cikin manyan ‘yan ta’addan da rundunar sojin saman Najeriya ta raunata a Sabon Tumbuns kusa da Kirta Wulgo a watan Fabrairun wannan shekarar. Samame da aka kai ta sama a cikin kwanaki da suka gabata na iya yin ajalinsa tare da wasu manyan ISWAP inda suke mummunar jinya ciki har da Abu Ibrahim al-Hashimi al. -Qurayshi,” majiyar tace
A yanzu haka, PRNigeria ta tattaro cewa an nada Mallam Bako Gorgore a matsayin sabon shugaban ISWAP wanda zai dasa daga inda Shuwaram ya tsaya.
A yayin da aka so jin ta bakin Kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce jiragen NAF tare da goyon bayan sojin kasa sun ci gaba da kai farmaki a Tumbuns, kusa da Kirta Wulgo a Marte da ke yankin tafkin Chadi, amma bai tabbatar da mutuwar Shuwaram ba. .
Gabkwet ya ce: “Ba na iya tabbatar da mutuwar kowanne shugaban ‘yan ta’adda. Ba ma so mu yi wata magana kan jita-jita. Duk da haka, sojojin mu a fagen fama tare da sauran hukumomin tsaro sun ci gaba da matsantawa shugabannin ‘yan ta’adda da yankunansu har sai mun kammala wannan aiki”.
Yaushe Shuwaram ya hau mulki
Majiyoyi sun tabbatar wa PRNigeria cewa Sani Shuwaram wanda ba a san shi ba ya maye gurbin Aba-Ibrahim, wanda kwamitin rikon kwarya na Abu-Mosab Albarnawi ya nada, sakamakon umarnin hedkwatar kungiyar IS da aka fi sani (ISIS), a watan Augustan na shekarar da ta gabata.
Alkali Bukar Arge ya rantsar da Shuwaram a wani dan karamin biki da aka yi a Kurnawa, wani sansani mai tazara a tafkin Chadi, wanda ake yi wa lakabi da hedkwatar ISWAP a Abadam a jihar Borno.
Idan za a tuna, mambobin Majalisar Shura ta ISWAP a watan Nuwamban 2021, sun tabbatar da nadin Shuwaram mai shekaru 45 a matsayin sabon shugaba (Wali) a yankin tafkin Chadi.
Asali: Legit.ng