Borno: An halaka mayakan ISWAP, sojoji sun dakile harin miyagu a sansanin soji
- Majiyoyi daga rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa dakarun Operation Hadin Kai sun halaka mayakan ISWAP masu yawa
- An gano cewa miyagun maharan sun kaddamar da farmaki kan sansanin soji da ke Doron Baga a Kukawa a ranar Asabar
- Bayan artabun, miyagun sun mutu, wasu sun jigata sannan daga bisani suka kwashe gawawwakin 'yan uwansu tare da tserewa ta Daban Masara, Madayi da Gratai
Borno - Wasu majiyoyin soji sun shaidawa jaridar TheCable cewa, dakarun Operation Hadin Kai sun kashe mayakan kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP) da dama a Borno.
An ce maharan sun kaddamar da harin ne a sansanin sojojin da ke Doron Baga a karamar hukumar Kukawa da sanyin safiyar Asabar.
Majiyoyi sun ce mayakan dauke da gurneti da manyan motocin bindigu 5 ba su samu galaba a kan sojojin.
An ce sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addan ne a wani artabu da aka kwashe kusan sa’o’i biyu ana gwabzawa.
Hakazalika wutar da sojojin suka samu, kamar yadda majiyoyi suka ce, ta yi sanadiyar kashe maharan da ba a tabbatar da adadinsu ba, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Daya daga cikin majiyar ta ce "An samu asarar rayuka sosai a bangaren maharan."
The Cable ta fahimci cewa, maharan sun kwashe gawarwakin mayakansu da wadanda suka jikkata ta hanyar Daban Masara, Madayi da Gratai.
Sansanonin sojoji a kodayaushe na zama abun hari ga miyagun da suka addabi yankin arewa maso gabas sama da shekaru goma.
Sai dai a watannin da suka gabata sojojin na ci gaba da kai farmaki kan maharan.
A ranar Juma’ar da ta gabata rundunar sojin kasar ta bayar da rahoton yadda dakarunta suka kashe ‘yan ta’addar ISWAP/Boko Haram da dama a kusa da kauyukan Ndufu da Musiri a Borno.
A cewar rundunar sojojin sun kwato makamai tare da kubutar da mazauna yankin 30 da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ta kuma kara da cewa dakarunta sun lalata sansanoni daban-daban na 'yan ta'addan yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin share fage.
Borno: Dakarun sojin Najeriya sun yi artabu da mayakan ISWAP, an yi musayar wuta
A wani labari na daban, a yammacin Litinin, rundunar sojin jihar Borno tayi musayar wuta da wasu da ake zargin mayakan ISWAP ne, a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Kamar yadda majiyoyin suka bayyana, musayar wutar ya dau kimanin minti 30, Daily Trust ta ruwaito.
An tattaro yadda Mayakan ISWAP suka auka wa anguwan Biu ta babban titi, kafin dakarun su yi nasarar dakile harin.
"Dakarun sun yi nasarar dakile harin a Damboa. Musayar wutar ta kai kimanin minti 25, kafin su tsere ta hanyoyi daban-daban," a cewar majiyar.
Asali: Legit.ng