Bidiyon yadda aka yiwa dan majalisar Neja ruwan duwatsu da ihun 'Ba ma yi' bayan ya ziyarci mazabarsa

Bidiyon yadda aka yiwa dan majalisar Neja ruwan duwatsu da ihun 'Ba ma yi' bayan ya ziyarci mazabarsa

  • Dan majalisa mai wakiltan karamar hukumar Magama ta jihar Neja ya sha da kyar a hannun al’umman mazabarsa
  • Mutanen mazabar tasa sun yi masa ruwan duwatsu a lokacin da ya kai ziyarar jaje sakamakon harin da yan bindiga suka kai yankin wanda ya yi sanadiyar kashe DPO
  • Hakazalika, mutanen sun yi masa ihun 'Ba ma yi' a lokacin da ya zo fita daga yankin

Niger - Hon. Musa Suleiman Nasko, dan majalisa mai wakiltan karamar hukumar Magama ta jihar Neja ya sha da kyar a hannun al’umman mazabarsa.

A wani bidiyo da shafin the_northern_trend_blog ya wallafa a Instagram, an gano yadda mutanen mazabarsa suka dunga jifarsa da duwatsu.

Bidiyon yadda aka yiwa dan majalisar Neja ruwan duwatsu a yayin da ya ziyarci mazabarsa
Bidiyon yadda aka yiwa dan majalisar Neja ruwan duwatsu a yayin da ya ziyarci mazabarsa Hoto: nairaland.com
Asali: UGC

An tattaro cewa lamarin ya faru ne bayan dan majalisar ya ziyarci mazabar tasa domin jajantawa mutanen garin Magama wadanda rikicin ‘yan fashin ya cika da su.

Kara karanta wannan

Ministan shari'a Malami: Ba zan yi murabus ba, sai na kammala wa'adin aiki na a mutunce

A garin Magama ne yan bindiga suka kashe jami’an tsaro ciki harda shugaban yan sandan yankin wato DPO mai kula da garin Nasko.

Yana a hanyarsa ta fita daga garin ne bayan ya gana da iyalai, shugabannin addini da yan sanda a Magama, lokacin da mutanen suka far masa da duwatsu.

A cikin bidiyon, an jiyo muryoyin wasu mutane suna fadin ‘Ba ma yi, Ba ma yi. Mu jefi Shege, dan shegiya kawai, Shege Dan Bura Uba! Ka chi Bura Ubanka! Ba Ma yi. Ku jefe shi.’

An kuma jiyo karar harbi wanda ake zaton masu tsaron dan majalisar ne ke yinsa a iska domin tarwatsa mutanen da suka kai masa farmaki.

Kalli bidiyon a kasa:

Yan bindiga sun harbe DPO, da wasu jami'an tsaro 6 a wani kazamin hari da suka kai Neja

Kara karanta wannan

Sun ji wuta: Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun kashe da yawa, wasu sun tsere

A baya, mun kawo cewa aƙalla jami'an tsaro bakwai suka rasa rayukansu ciki har da shugaban ofishin yan sanda (DPO) na caji Ofis ɗin Nasko, ƙaramar hukumar Magama, jihar Neja, a harin yan bindiga ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana a yau Talata, 15 ga watan Maris.

Yan bindigan sun yi yunkurin kai hari kan jam'an ƙauyen Nasko, amma jami'an tsaro da suka haɗa da yan sanda, sojoji, da yan Bijilanti suka tarbe su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng