Kano: Yadda Alkali Aminu Gabari ya karbi cin hancin zunzurutun kudi daga mai korafi
- Ana zargin babban alkalin kotun majistare a jihar Kano, Aminu Gabari, da kalmashe N400,000 daga wurin mai kara na cin hanci
- Gabari ya yi kaurin suna wurin daurewa da sanya sharudda masu tsauri kan masu suka ko caccakar Gwaman Abudllahi Ganduje na Kano
- Masu shiga da kara sun shaida cewa, duk wata harkallar masu kudi ko kuma shari'ar da ta shafin manyan mutane ko masu kudi kotunsa ake mika ta
Kano - Wani babban alkalin jihar Kano, Aminu Gabari, an zarge shi da tilasta wa wani mai kara a wata kara da ke gaban kotunsa biyan kudi N400,000 a asusunsa a matsayin cin hanci.
Gabari ya yi kaurin suna wajen daurewa da kuma sanya wasu tsauraran sharuddan belin ga masu sukar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.
Daily Nigerian ta tattaro cewa korafe-korafe da ke fitowa daga gidan gwamnatin Kano a koda yaushe ana shigar da su tare da gurfanar da su a gaban kotun sa, wanda hakan ya sabawa sashe na 107 (4)(5)(6) na dokar shari’a ta gwamnati, ACJL.
Dokar ta tanadi cewa alkalai a kotunan da ake shigar da kararraki kai tsaye bai kamata su zama wadanda za su yi shari'a ba sai dai kawai su gane laifin da aka aikata sannan su mika lamarin ga wani alkali.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Masu shigar da kara sun kuma shaidawa Daily Nigerian cewa “harkallar masu kudi” da suka shafi manyan mutane ko makudan kudade ana kai su kotunsa, saboda dalilan da suka fi sani da bangaren shari’a na jihar.
A wata kara da ya shigar gaban alkalin alkalan Kano, Nura Sagir, wani Ismail Maitama Yusuf (mai kara a gaban Mista Gabari) ya yi ikirarin cewa ya biya kudi naira 400,000 kashi biyu ga Mista Gabari domin a sako wani bangare na kudinsa da aka ajiye a kotu.
Takardar karar mai dauke da kwanan watan 31 ga watan Janairu, 2022, ta bayyana yadda Gabari ya saki wasu mutane biyu da ake zargi da laifin damfarar mai kara Naira miliyan 38.
Da Daily Nigerian ta tuntubi Gabari don yin magana a kan zargin, alkalin kotun ya musanta karbar wani cin hanci daga wanda ya shigar da karar, inda ya ce zargin adawa ce kawai.
A cewar Gabari, wanda ya shigar da karar ya fito da wadannan zarge-zargen ne domin a tausaya masa saboda kotu ta bayyana cewa tana nemansa.
Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri
A wani labari, a ranar Asabar, mummunar gobara ta tashi inda ta kone kadarorin miliyoyin naira a kwalejin First Ladies da ke Mariri a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.
Ana amfani da ginin ne a matsayin wurin adana kayayyaki na hukumar taimakon gaggawa, SEMA na jihar Kano, kuma gobarar ta taba wasu sassan makarantar, Daily Trust ta ruwaito.
A yayin bada labarin, sakataren SEMA, Dr Saleh Aliyu Jili ya ce kayan rage radadin sun hada da katifu da matasan kai 900, injinan markade, keken dinki, injinan faci, omon wanki da sauransu duk gobarar ta lamushe.
Asali: Legit.ng