Rashin wutar lantarki ce matsala mafi girma ga cigabar kasar nan, Tinubu

Rashin wutar lantarki ce matsala mafi girma ga cigabar kasar nan, Tinubu

  • Dan takaran kujeran shugaban kasa ya bayyana abu daya dake hana tattalin arzikin Najeriya cigaba
  • Tinubu ya ce idan ya zama shugaban kasa, zai karfafa masana'antu saboda muhimmancinsu ga tattalin arziki
  • Tinubu ya zayyana jerin abubuwa bakwai da zai mayar da hankali kansu idan ya lashe zaben 2023

Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa zai farfado da tattalin arzikin Najeriya tare da rage dogaro kan arzikin man fetur.

Dan takaran kujeran shugaban kasan ya ce ya yi niyyar gadar kujerar shugaba Muhammadu Buhari ne don amfanin yan Najeriya, rahoton Guardian.

Tinubu
Rashin wutar lantarki ce matsala mafi girma ga cigabar kasar nan, Tinubu
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Ku samar da sashin harkokin siyasa don tallata yan uwanku Musulmai, Tinubu ga shugabannin Musulunci

Tinubu yace rashin wutar lantarki ne babban matsala ga cigaban tattalin arzikin Najeriya saboda rashin wuta ke kara farashin kaya, hana mutane aiki cikin nishadi, da kuma kawo tasku ga samar da ayyukan yi.

Yace:

"Ingila, Amurka da Sin sun aiwatar da tsare-tsare don kare masana'antunsu, samar da ayyukan yi, da fitar da kaya. Wadannan kasashe sun daura kansu kan turban nasara a yau da gobe."
"Wajibi ne mu yaki wadannan kayoyin dake hanamu samun ingantaccen wutan lantarki."

Mun cire tallafin lantarki a boye gaba daya, zamu cire na man fetur: Gwamnati ga IMF

Ministar kudi da kasafin kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta cire tallafin wutan lantarki gaba daya a boye, kuma tana shirin cire na man fetur.

Hajiya Zainab, ta bayyana hakan ne a taron asusun lamunin duniya (IMF) da ya gudana ta yanar gizo.

Ta ce karin farashin danyen mai a kasuwar duniya na kara yawan kudin tallafin da gwamnatin tarayya ke biya.

Kara karanta wannan

Da gaske ne, mun cire tallafin wutar lantarki ta hanyar kara kudin wuta, Hukumar NERC

Zainab tace sun fara cire tallafin da gwamnati ke badawa amma an samu koma baya ne, A Yulin shekarar nan ya kamata a cire na mai amma jama'a suka yi ca.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng