Matar Tsohon Shugaban Biafra Ta Faɗi Dalilin Da Yasa Ta Shararawa Matar Gwamna Mai Barin Gado Mari
Jihar Anambra - Ambasada Bianca Ojukwu, matar marigayi Cif Chukeuemeka Ojukwu, ta bayyana abin da ya faru tsakanin ta da tsohuwar First Lady ta Jihar Anambra, Ebelechukwu Obiano.
Yayin taron rantsuwar kama aiki na Gwamna Charles Soludo, a ranar Alhamis, Ebelechukwu Obiano da Bianca sun yi rikici.
Lamarin ya janyo hankulan yan Najeriya da dama a dandalin sada zumunta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga bisani Soludo ya nemi afuwar al'ummar Anambra da bakin da suka hallarci taron, yana mai cewa rashin jituwa ne tsakanin mutanen biyu ya janyo hakan.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Juma'a, Bianca ya magantu kan abin da ya faru.
"A yayin da aka fara bikin rantsar da Farfesa Charles Soludo da mataimakinsa kuma dukkan baki sun zauna, tsohuwar First Lady na Jihar Anambra, Mrs Ebele Obiano, bata iso ba. Daga bisani ta iso bayan awa daya da rabi da fara bikin. Ban nuna alamar na san ta iso ba.
"Abin mamaki, ta taho inda na ke zaune ina tunanin ta zo ta gaishe ni ne. A maimakon hakan, tana isowa sai ta fara zagi na tana daga murya, tana zolaya ne tana tambayar mene na zo yi a wurin tana amfani da munanan kalamai da ba za a iya rubutawa a jarida ba.
"Ta tambaya idan na zo in yi murnar ranar su na karshe a kan mulki ne. Amma ban kula ta ba. Daga nan, ta cigaba da saka hannunta a kafada na tana daga murya. Ni kuma, ban kula zagin da ta ke min ba bisa shawarar wadanda suke zaune kusa da ni, sau biyu na ce ta dena taba ni da hannunta.
"Ta cigaba da taba ni har ta kara da damkar kallabi na, ta yi yunkurin cizgewa amma ba ta yi nasara ba. Wannan abin da ta aikata cin mutunci ne ga mai sarauta iri na a kabilar igbo,' in ji ta.
Ta cigaba da cewa:
"A wannan lokacin ne na mike tsaye domin in kare kai na kuma na sharara mata mari domin hana ta kai min hari. Da ta matso kusa da ni, na cizge gashin kwalliyarta. Ta rike gashin da hannu biyu ta yi kokarin kwacewa daga hannu na.
"Tsohon shugaban jam'iyyar APGA, Umeh (Cif Victor Umeh), ya umurci ta kyalle ni kuma ya umurci mambobin APGA da ke wurin su tafi da ita, suka tafi da ita wurin da mijinta Cif Willie Obiano ya ke zaune, ta zauna shiru har aka gama abin.
"Abin da ya bani mamaki shine bisa dukkan alamu a buge da giya ta ke. Na yi mamakin jin warin giya a numfashinta a irin wannan lokacin. Ta yaya first lady za ta yi tatil da giya ta zo wurin taron rantsarwa da aka fara karfe 9 na safe?
"Abin takaici ne yadda ta zubar da mutunci ta aikata irin wannan abin a wurin taro na jiha. Hakan bai yi wa Gwamna dadi ba, hakan yasa bai jima ba ya dauke ta suka bar wurin.
"An yi sa'a, abin bai janyo tsaiko a taron da ake yi ba kuma na tsaya har sai da aka gama taron da ni sannan daga bisani muka yi taron cin abinci a Gidan Gwamnati."
Asali: Legit.ng