Yadda Buhari da Gwamnoni suka karbo bashin Naira Tiriliyan 6.64tr a cikin shekara daya

Yadda Buhari da Gwamnoni suka karbo bashin Naira Tiriliyan 6.64tr a cikin shekara daya

  • Gwamnonin jihohi da Gwamnatin tarayya sun nemo aron Naira Tiriliyan 6 a shekarar da ta wuce
  • Shugabar DMO mai kula da bashin Najeriya ta ce duk da haka, bashin da ake ci bai yi yawa sosai ba
  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta biya bashin N1.03tr a cikin watannin ukun farkon shekarar 2021

Abuja - A ranar Alhamis, 17 ga watan Maris 2022, ofishin DMO mai kula da bashi a Najeriya ya ce bashin da ke kan wuyan gwamnati sun karu sosai a 2021.

Punch ta rahoto Darekta-Janar ta DMO, Patience Oniha ta na cewa kudin da ake bin Najeriya ya karu daga N32.92tr a 2020 zuwa N38.56tr a shekarar 2021.

Patience Oniha tayi wannan bayani a lokacin da ta zanta da manema labarai a Abuja. Oniha ta ce wannan ya kunshi bashin gwamnatin tarayya da na jihohi.

Kara karanta wannan

Farashin lantarki ya tashi bayan Gwamnati tayi wuf, ta dakatar da tallafin wuta

An yi amfani da wannan bashi da aka karbo wajen cike gibin da aka samu a kasafin kudi tare da yin ayyukan more rayuwa da kuma farfado da tattalin arziki.

Bashin bai yi yawa ba

Duk da yawan bashin da ake ganin gwamnatin kasar nan ta na ci, shugabar ta DMO ta ce har yanzu idan aka kamanta yawan bashin da GDP, 22% ne rak.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bankin Duniya ya kayyade cewa ka da nauyin bashin kasa ya zarce 55% na jimillar tattalin arzikinta. Kungiyar ECOWAS kuwa ta tsaida shi ne a kan 70%.

DMO DG
Patience Oniha Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Za mu fadada samun kudin shiga

Jaridar Daily Trust ta ce a shekarar bara, an ci bashi ne daga tsarin Eurobonds da Sukuk da sauransu. An yi amfani da kudin domin ayi wa jama’a ayyuka.

Darekta-Janar ta DMO ta ce an kawo dokar Finance Act 2019 ne da nufin a kara yawan abin da ake samu ta haraji domin ganin an rage dogara da karbo bashi.

Kara karanta wannan

Kudi sun samu: Najeriya ta sayar da danyen mai na N14.4trn a 2021 ga wasu kasashe 5

“Gwamnatin tarayya ta na lura da nauyin bashi ga kudin shigan gwamnati, kuma ta fara daukar matakan kara samun haraji da aka shigo da dokar kudi tun 2019.”

- Patience Oniha

Kudi sun tafi wurin biyan bashi

Bayanan da aka fitar ya nuna an kashe N612bn wajen biyan bashin gida tsakanin Junairu zuwa Maris a 2021. An kuma biya $1bn na bashin da aka karbo a waje.

Tsakanin Afrilu zuwa Yunin 2021, an kashe fiye da N447bn domin a biya bashi a gida da waje. Sannan an kashe N1.03tr da N429bn tsakanin Yuli zuwa Disamba.

Ganguna 100m sun bace

A makon nan aka ji bincike ya nuna shugaban NNPC Limited yana bukatar ya yi karin bayani a kan inda gangunan mai miliyan 109 suka shiga a shekarar 2019.

Binciken da ofishin AuGF ya gudanar a 2019 ya nuna shugaban kamfanin NNPC yana da aiki a gabansa. Akwai alamar tambaya a kan kudin da aka zuba a FAAC.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng