Yan Boko Haram sun sace Likita daya tilo dake asibitin Gubio, jihar Borno
- Yan ta'adda sun shiga garin Gubio sun yi awan gaba da babban Likitan karamar hukumar
- Jama'ar garin sun bayyana cewa yan ta'addan basu dauki komai ba illa Likita Bulama
- Shugaban karamar hukumar Gubio, Bukar Zulum Zowo, ya tabbatar da labarin
Borno - Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari karamar hukumar Gubio dake jihar Borno inda suka yi awon gaba da Likita daya tilo dake garin, Geidam Bulama.
Mazauna garin sun bayyana cewa yan ta'addan sun dira garin ne cikin motar Hilux da babura kuma suka tafi gidan Likitan kai tsaye misalin karfe 2 na dare.
Sun kara da cewa yan bindigan basu dauki komai ko kashe kowa ba, Likitan kawai suka dauke..
Wani mazauni mai suna Mohammed Usman Shettima ya ce bayan mintuna 30 da dauke Likitan, yan bindigan suka dawo suka bankawa gidaje 74 wuta, amma ba'ayi rashin rai ba.
Yace:
"Gidan Likitan bai da nisa ga hedkwatar yan sanda da kuma barikin Sojoji dake cikin garin Gubio. Abin takaici ne lamarin tsaro ya fara tabarbarewa a Guno, mun fara samun hare-haren Boko Haram."
Shugaban karamar hukumar Gubio, Bukar Zulum Zowo, ya tabbatar da labarin amma yace ba yan ta'adda suka bankawa gidaje wuta ba, yace gobara ce.
Yayinda aka tuntubi kwamishanar lafiyar jihar, Mrs Juliana Bitrus, ta bayyana cewa:
"Lallai na samu labari da safen nan (Laraba) cewa an sace Dakta Bulama. Muna iyakan kokari da hukumomin tsaro don ceto shi."
Yan Bindiga Sun Bindige Mataimakin Shugaban Kungiyar Dilallan Katako a Borno
A wani labarin kuwa, wasu ‘yan bindiga sun harbe mataimakin shugaban kungiyar sarrafa katako ta Jihar Borno, Mr Aga City, Vanguard ta ruwaito.
City, kamar yadda ake kiransa, dan asalin karamar hukumar Gwoza ne da ke cikin jihar.
Majiyoyi sun bayyana yadda marigayin yake zaune a Shagari low-cost kusa da Maimalari Cantonment a garin Maiduguri.
An harbe shi ne yayin da ya ke gab da shiga motar sa, kirar Corolla bayan ya siya wa iyalin sa taliya zai wuce gida.
Wani abokin mamacin wanda ya bukaci a sakaya sunan sa ya sanar da wakilin Vanguard cewa lamarin ya yi matukar firgita jama’a.
Asali: Legit.ng