Da gaske ne, mun cire tallafin wutar lantarki ta hanyar kara kudin wuta, Hukumar NERC

Da gaske ne, mun cire tallafin wutar lantarki ta hanyar kara kudin wuta, Hukumar NERC

  • Hukumar dake da hakkin lura da lantarkin Najeriya ta tabbatar da cewa an cire tallafin wuta gaba daya
  • Duk da rashin wutan da yan Najeriya ke fama da shi, an kara musu kudin wutan da zasu rika biya
  • Ministar kudi tuni tace kamar yadda aka cire tallafin wuta, da sannu haka za'a cire na man fetur

Abuja - Hukumar lura da wutar lantarkin Najeriya NERC ta tabbatar da labarin cewa gwamnatin tarayya ta cire tallafin wutar lantarki kuma an kara kudin wuta.

Shugaban hukumar, Mr Sanusi Garba, ya bayyanawa manema labarai a Abuja cewa an yi hakan ne bisa tsarin da akayi na kara kudin wuta bayan kowani wata shida, rahoton ChannelcTV.

Garba yace hakkin hukumomin rarraba wuta ne su sanar da kwastamominsu cewa an kara kudin wuta.

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Wannan na faruwa ne lokacin da wutar kasar ta lalace kusan kwanaki biyu a jere.

Garba yace wutar ta samu matsala ne saboda fasa bututun mai da ake yi da kuma lalacewar layi 330KV dake Ughelli.

Da gaske ne, mun cire tallafin wutar lantarki ta hanyar kara kudin wuta, Hukumar NERC
Da gaske ne, mun cire tallafin wutar lantarki ta hanyar kara kudin wuta, Hukumar NERC
Asali: Facebook

Mun cire tallafin lantarki a boye gaba daya, zamu cire na man fetur: Gwamnati ga IMF

Ministar kudi da kasafin kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta cire tallafin wutan lantarki gaba daya a boye, kuma tana shirin cire na man fetur.

Hajiya Zainab, ta bayyana hakan ne a taron asusun lamunin duniya (IMF) da ya gudana ta yanar gizo.

Ta ce karin farashin danyen mai a kasuwar duniya na kara yawan kudin tallafin da gwamnatin tarayya ke biya.

Zanaib tace sun fara cire tallafin da gwamnati ke badawa amma an samu koma baya ne, A Yulin shekarar nan ya kamata a cire na mai amma jama'a suka yi ca.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng