Yan sanda da Sojoji sun yi artabu da yan bindiga a Abuja, sun ceto mutum ɗaya
- Jami'an tsaro sun ɗanɗana wa yan bindiga wuta a hannu yayin da suka yi yunkurin garkuwa da wani mutum a Abuja
- Dakarun yan sanda, Sojoji da kuma Yan Bijilanti suka tarbi yan ta'adda, aka yi musayar wuta har suka tsere
- Kakakin yan sanda na Abuja ta bayyana cewa jami'an sun damƙe wani ɗan shekara 18 da ake zargin yana daga cikin maharan
Abuja - Jami'an yan sanda na birnin tarayya Abuja da haɗin guiwar Sojoji sun dakile yunkurin garkuwa a yankin Dobi Kwalita dake Gwagwalada.
Kakakin yan sandan Abuja, DSP Josephine Adeh, ita ce ta sanar da haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ta ce jami'an tsaro sun samu nasarar dakile harin da kuma ceto mutumin da aka so sacewa bayan samun bayanan sirri daga mazauna Dobi kwalita.
Vanguard ta rahoto a sanarwan, kakakin yan sandan ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Mutanen yankin sun fara zargin tattaruwar wasu baƙi da suke ganin masu garkuwa ne ranar Talata. Bayan samun rahoto nan take yan sanda da taimakon sojoji suka kai ɗauki."
Adeh ta ƙara da cewa dakarun Bataliya ta 176 da kuma yan Bijilanti suka dira yankin cikin gaggawa domin kai ɗauki.
"A yunkurin neman hanyar sulalewa, yan ta'addan suka gwabza da jajirtattun jami'an tsaro, kuma nan da nan suka dakile harin."
"Yayin haka suka samu nasarar ceton wani mazaunin Dobi Kwalita, Sani Dauje, haka nan kuma suka damƙe wani da ake zargin yana cikin maharan ɗan shekara 18."
Kakakin yan sanda ta yi bayanin cewa yanzu haka wanda aka kama na hannun jami'an sashin bikciken manyan laifuka CID domin tsananta bincike.
A cewarta, jami'an sun baza komar su ta ko ina a wani yunkuri na kame ragowar yan tawagar masu garkuwa da mutane.
A wani labarin na daban kuma Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya
A makon da ya gabata, yan ta'adda sun zafafa kai hare-hare kan jami'an tsaro da yan kasa nusamman a arewacin Najeriya.
Mun tattaro muku yadda aka kashe aƙalla mutum 103 a faɗin Najeriya cikin mako guda, wanda ya haɗa za jami'an tsaro 24.
Asali: Legit.ng