Da duminsa: Ku bari Buni ya gudanar da taron gangamin jam'iyyar APC, Buhari ya aike da wasika
- Bayan haduwa da Buni, Shugaba Buhari ya bukaci daukacin yan jam'iyyar APC su bar Buni ya sha iska
- Shugaban kasan ya bayyana haka a wasikar da ya aikewa gwamnonin jam'iyyar ta APC
- Kun ji a baya cewa wasu jiga-jigai na APC zasu tafi Landan ganin shugaba Buhari kan lamarin rikicin APC
Landan - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a bari gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya gudanar da taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
A wasikar da ya aikewa Shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, Buhari yace gudun shiga rikice-rikicen kotu, a bari Buni ya karasa aikinsa.
Buhari yace:
"Na samu labarin cewa sakamakon abubuwan da suka faru, APC na fuskantar kasa-kasai a kotu a fadin tarayya."
"Sakamakon haka, akwai yiwuwan hukumar INEC ta hana jam'iyyar gudanar da ayyukanta."
"Tun da jam'iyyar ta gaza canza shugabannin kwamitin rikon kwaryan, dubi ga lokaci ya kamata abi ka'idar da INEC tace na sanar da ita cikin isasshen lokaci kafin ayi taron gangamin."
"Ko shakka babu akwai rikice-rikice, wanda ka iya haifar da matsaloli ta yadda INEC zata yi watsi da ayyukan jam'iyyar, zabenta da kuma komai nata."
"Saboda haka, a bari Mai Mala Buni da sauran mambobin kwamitinsa su cigaba da shirye-shiryen taron gangamin ranar 26 ga Maris, 2022."
Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari
Wannan ya biyo bayan zuwar Gwamna Mai Mala Buni Landan don ganin Shugaba Muhammadu Buhari.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi takakkiya daga Dubai, kasar UAE zuwa Landan don ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 16 ga Maris 2022.
Gwamnan wanda shine Shugaban kwamitin rikon kwarya ya tafi Landan daga Dubai inda yake jinya don ganin Buhari bisa tsigeshi da akayi daga kujerarsa shugaban jam'iyyar.
Asali: Legit.ng