Yakin Rasha da Ukraniya: An kashe yan jaridan Fox News biyu, an cirewa daya kafa
- Ana cigaba da kashe yan jarida masu aikin daukp rahoton yakin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine
- Kisan dan jarida dake bakin aiki babban laifi ne na yaki a idon kotun duniya
- Yayinda yan jarida biyu suka rasa rayukansu, mutum daya ya sha da kyar amma ya rasa wanni sashen jikinsa
Dan jaridan tashar Fox News dake Amurka, Benjamin Hall, ya rasa kafarsa guda yayinda aka bude musu wuta lokacin da suke daukan rahoto kan yakin dake gudana a Ukraine.
Anton Gerashchenko, mai baiwa Ministan harkokin cikin gidan a kasar Ukraine, ya bayyana hakan ranar Talata a shafinsa na Telegram.
Yace an kwantar da dan jaridan a asibiti bayan budewa motarsu wuta tare da abokan aikinsa kuma an kashe biyu cikinsu a Kyiv.
Yan jaridan da aka kashe sun hada da Pierre Zakrevsky, da Oleksandra Kurshynova.
Gerashchenko ya ce mutum daya da ya tsallake rijiya da baya.
Hakazalika ma'aikatar tsaron kasar Ukraine ta tabbatar da labarin a jawabin da ta saki a shafinta na Tuwita inda tace:
"Gaskiya ake yaka. Sojojin Rasha sun budewa yan jaridar Fox News wuta kusa da Kyiv. Mai daukan hoto Pierre Zakrevsky da Oleksandra Kurshynova sun mutu. Banjamin Halla ya tsallake rijiya da baya amma an cire kafarsa."
Mun hakura da shiga kungiyar NATO: Shugaban kasar Ukraine
Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky , a ranar Talata ya bayyana cewa kasarsa ta hakura da shiga cikin kungiyar NATO, babban dalilin da yasa Rasha ta fara yakin nan.
A hirar da yayi da rundunar Sojin gaggawa karkashin Birtaniya, Zelensky yace da alamun zasu hakura tunda an fada musu ba zasu iya shiga ba, rahoton Aljazeera.
Kungiyar NATO (North Atlantic Treaty Organization) wata kungiyar kasashen 30 (Turai 28 da Amurka da Kanada) ne da aka kafa na hada karfi da karfe.
An kafa kungiyar bayan yakin duniya na biyu kuma an kafa ta ranar 4 ga watab Afrilu, 1949.
Duk mamban kungiyar da wani ya kaiwa hari ya tono tsokanar sauran kasahen talatin.
Asali: Legit.ng