Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun halaka jami'an tsaron gidan gyaran hali a Imo

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun halaka jami'an tsaron gidan gyaran hali a Imo

  • Yan bindiga sun yi wa Gandurobobi kwantan bauna a jihar Imo, sun halaka aƙalla mutum biyu sun jikkata wasu da dama
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun yi amfani da Nakiya wajen fatattakar ɗaya daga cikin motocin jami'an
  • Hukumar gyaran hali ta Najeriya reshen Imo ta ce a halin yanzun tana tattara bayanai kan abinda ya faru kafin ta sanar

Imo - Jami'an tsaron gidan gyaran Hali guda biyu sun rasa rayukansu a hannun yan bindigan da ba'a san ko suwaye ba a garin Okigwe, jihar Imo.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa harin wanda ya faru a yankin Umulolo dake garin da safe ya bar mutane cikin tashin hankali.

Wani jami'in tsaro, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya shaida wa manema labarai cewa yan bindigan sun mamayi jami'an gidan Yari ne ba zato ba tsammani.

Kara karanta wannan

Yakin Rasha da Ukraniya: An kashe yan jaridan Fox News biyu, an cirewa daya kafa

Taswirar Imo
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun halaka jami'an tsaron gidan gyaran hali a Imo Hoto: punchng.com
Asali: UGC

The Nation ta rahoto Jami'in ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yan bindiga sun farmaki motocin Hilux biyu ɗauke da jami'an gidan Yarin jihar Imo ranar Laraba da safe a dai-dai Umulolo Okigwe kuma maharan sun jefa wa motocin nakiya."
"Nan take mutum biyu suka rasa rayukansu wasu kuma na kwance a Asibiti. Nakiyar da suka dasa ta yi ragaraga da Mota ɗaya, ɗayar kuma abun be shafe ta ba."
"Yanzu haka an ɗakko Motar da bata yi komai ba an maida ta hedkwata dake Owerri. Jami'an da lamarin ya faru da su suna cikin dakarun Operation Search and Flush da gwamnatin Imo ta kafa domin magance miyagu."

Ya kuma ƙara da cewa jami'an sun fito ne daga Owerri tun safe, amma suna isa Okigwe, yan bindigan suka mamaye su, suka farmake su ba zato ba tsammani.

Kara karanta wannan

Mafarauci ya bindige tsohon shugaban APC har Lahira, ya ce ya ɗauka wata dabba ce

Wane mataki hukumar ta ɗauka?

Yayin da aka tuntuɓi kakakin hukumar jami'an gyaran hali, wanda aka fi sani da Ganduroba na jihar Imo, Goodluck Uboegbulem, ya ce:

"Har yanzun muna binciken gano ainihin abinda ya faru, da zaku ƙara hakuri zuwa anjima zan baku cikakken bayani."

A wani labarin kuma Jirgin yakin NAF ya yi luguden wuta a wurin shagalin auren kasurgumin ɗan bindiga, rayuka sun salwanta

Jirgin yaƙin rundunar sojin sama ya yi luguden wuta kan wurin shagalin bikin wani kasurgumin ɗan bindiga a Katsina.

Bayanai sun bayyana cewa luguden wutan ya yi wa yan ta'adda mummunan ɓarna, ya tura manyan su barzahu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262