Mafarauci ya bindige tsohon shugaban APC har lahira a jihar Enugu bisa kuskure
- Wani maharbi ya bindige tsohon shugaban jam'iyyar APC na wata gunduma a jihar Enugu bisa kuskure ranar Asabar
- Jama'an gari sun ɗora wa Fulani makiyaya laifin, amma daga baya aka gano cewa wani Mafarauci ne ya aikata kisan
- Hukumar yan sanda ta jihar ta ce tuni jami'ai suka fara bincike a sashin CID kasancewar lamarin ya shafi kisan kai
Enugu - Wani Mafarauci ya harbe tsohon shugaban APC na gundumar Akpa-Edem, ƙaramar hukumar Nsukka jihar Enugu, Chibueze Omeje, har lahira ranar Asabar, yayin da yake aiki a gonarsa a Edem.
Vanguard ta rahoto cewa Mafaraucin mai suna Monday Oriewu, bayan harbe shugaban APCn, ya bar gawarsa a cikin gona kuma ya kama gabansa.
Wasu mazauna yankin da suka nemi a sakaya sunan su, sun bayyana cewa mutanen ƙauyen sun yanke cewa Fulani Makiyaya ne suka aikata wannan ɗanyen aiki.
Jirgin yakin NAF ya yi luguden wuta a wurin shagalin auren kasurgumin ɗan bindiga, rayuka sun salwanta
Amma daga baya dattawan yankin suka gano cewa Oriewu ne ya aikata wannan ɗanyen aiki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahotanni sun bayyana cewa manyan mutanen garin suka haɗa wasu, aka je har gidan Mafaraucin kuma aka gano bindigar da ya yi amfani da ita.
Mafaraucin da ake zargin ya amsa laifinsa, amma ya ce ba da gan-gan ya aikata ba, ya hangi mamacin ne kamar wata dabba.
Wane mataki hukumomi suka ɗauka?
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Enugu, Daniel Ndukwe, yace abun da ya faru ya shafi aikata kisan kai kuma tuni yan sanda suka fara bincike.
Ya ce:
"Lamari ne da ya shafi kisan kai, wanda ake zargi Monday Oriewu ya kawo kan shi wurin yan sanda kuma aka tsare shi, bayan ya yi ikirarin bindige Omeje Chibueze har lahira bisa tunanin wata dabba ce."
"Ya faɗa mana lamarin ya faru a wannan rana yayin da ya fita Farauta da safe. Yanzu haka dai bincike na hannun CID na jihar Enugu."
A wani labarin na daban kuma Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya
A makon da ya gabata, yan ta'adda sun zafafa kai hare-hare kan jami'an tsaro da yan kasa nusamman a arewacin Najeriya.
Mun tattaro muku yadda aka kashe aƙalla mutum 103 a faɗin Najeriya cikin mako guda, wanda ya haɗa za jami'an tsaro 24.
Asali: Legit.ng