Karar kwana: An shiga jimami yayin da tsohon Sanatan Najeriya ya rasu a asibitin Landan

Karar kwana: An shiga jimami yayin da tsohon Sanatan Najeriya ya rasu a asibitin Landan

  • An ba da rahoton mutuwar dan kasuwa kuma dan siyasa, Sanata Patrick Enebeli Osakwe a birnin Landan
  • Wani jami’in gwamnatin jihar Delta Ossa Ovie Success ne ya sanar da mutuwar fitaccen dan siyasar a shafin sada zumunta
  • Osakwe wanda ya rasu yana da shekaru 73 a duniya ya wakilci yankin Delta ta Arewa a majalisar dattawa har sau biyu

Landan, Burtaniya - Tsohon Sanata mai wakiltar yankin Delta ta Arewa a majalisar dattawa Sanata Patrick Osakwe ya rasu, AIT ta ruwaito.

Ossai Ovie Success, mai taimaka wa gwamnan jihar Delta kan harkokin yada labarai, Ifeanyi Okowa ne ya sanar da rasuwar Osakwe a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 15 ga watan Maris.

Sanat Patrick Osakwe ya rigamu gidan gaskiya
Yanzu-Yanzu: Sanatan Najeriya Patrick Osakwe ya rasu a asibitin Landan | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Ya rubuta:

Kara karanta wannan

Mun saduda, mun hakura da shiga kungiyar NATO: Shugaban kasar Ukraine

"Mun rasa Sanata Patrick Osakwe. Ina mika ta'aziyyata ga iyalansa da al'ummar Ndokwa. Sanata Osakwe ya rasu ne a asibitin Landan da Yammacin yau yana da shekaru 73 a duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Patrick Enebeli Osakwe tsohon sanata ne da ya wakilci yankin Delta ta Arewa a jihar Delta.
"Ya zama dan majalisar dattawan Najeriya a 1999 kuma an sake zabansa a 2003 da 2007."

Kawo yanzu dai ba a iya tantance ainihin musabbabin mutuwar Osakwe ba saboda har yanzu iyalan mamacin ba su bayar da sanarwar mutuwarsa a hukumance ba.

Tsohon sanatan Najeriya ya rasu bayan ‘yar gajeriyar rashin lafiya

A wani labarin na daban, Nuhu Aliyu, tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Neja ta Arewa a majalisar dattawa, ya rasu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Aliyu wanda ya kasance mataimakin sufeto janar na 'yan sanda mai ritaya ya rasu a ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, bayan gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 79 a duniya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tinubu zai gana da Sanatocin jam'iyyar APC a yau dinnan

Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da mutuwar tsohon dan majalisar. Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana rasuwar Aliyu a matsayin babban rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: