Yan sanda sun damke Soji 2 da wasu mutum biyu suna fashi da makami

Yan sanda sun damke Soji 2 da wasu mutum biyu suna fashi da makami

  • Wasu yan fashi da makami sun kai hari shagon mai PoS don sace kudi kuma an hallaka mutum daya
  • Bincike ya nuna da Sojoji biyu aka kai harin kuma tuni sun shiga hannu tare da abokansu
  • Kwamishanan yan sandan Borno Umar ya kara da cewa cikin watanni biyar da suka wuce, barayi na kaiwa masu PoS hari a Maiduguri.

Maiduguri - Hukumar yan sanda a jihar Borno sun damke mutum biyar, ciki har da Sojoji biyu kan laifin fashi da makami da kisan kai.

Kwamishanan yan sandan jihar, Abdu Umar, ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a ranar Laraba a Maiduguri cewa sun yiwa wani mai shagon PoS mai suna Yusuf Usman, fashi.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 8 da Hukumar Kwastam ta hana fitar da su zuwa kasashen waje

Umar yace a fashin da ya auku ranar 6 ga Febrairu a kasuwar GSM, Bulumkutu, sun harbe wani mutum kuma sun raunata wani.

Pos thief
Yan sanda sun damke Soji 2 da wasu mutum biyu sun fashi da makami
Asali: Instagram

Yace da farko jami'ansa sun damke mutum uku– Mustapha Lawan, alias Bakura Dantawaye, Abubakar Mohammed, alias Bro Shagi, da Umar Ibrahim.

Su ukun sun bayyana cewa lallai sun aikata laifin tare da wani mutum biyu wadanda Sojoji ne Pte lgogo Michael da Pte Jibrin Adamu.

Umar da hukumar yan sanda da hukumar yan sandan gida Soja (Military Police) sun damke Sojojin biyu ranar Lahadi kuma sun amince sun aikata laifin.

Yace:

"An kai Sojojin biyu kotun soji gabanin turasu hedkwata da karin bincike."

Umar ya kara da cewa cikin watanni biyar da suka wuce, barayi na kaiwa masu PoS hari a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Daukar fansa: Fusatattun matasa sun far wa matafiya a wani yankin Kaduna

An damke dan sandan bogi yana amfani da kayan sarki wajen damfarar mutane

A wani labarin kuwa, jami'an hukumar yan sanda a jihar Kano sun damke wani dan sandan bogi wanda ake zargi da damfarar yan kasuwa ta hanyar Transfa na karya.

Matashin mai suna Yusuf Abdullahi, ya shiga hannu ne bayan wasu daga cikin yan kasuwan da ya damfara suka kai kararsa ofishin hukumar yan sanda.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana wannan matashi a bidiyo tare da yi masa tambayoyi

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng