Rashin wuta ya jawo an koma dogara da Janaretoci har a fadar Shugaban kasar Najeriya

Rashin wuta ya jawo an koma dogara da Janaretoci har a fadar Shugaban kasar Najeriya

  • Bayin Allah da ke zaune a gida da ‘yan kasuwa su na fama da matsanancin wahalar wutar lantarki
  • Wannan matsalar ta jawo abubuwa sun yi cak har a gwamnati, ma’aikata sun gaza yin aiki da kyau
  • Wani rahoto ya nuna yadda fadar shugaban kasa ta dogara da janerotoci domin a samu hasken lantarki

FCT AbujaWani rahoto da ya fito daga jaridar nan ta BusinessDay ya bayyana irin wahalar wutar lantarkin da ake fama da ita yanzu a fadin Najeriya.

Abin da aka fahimta shi ne har a fadar shugaban kasa watau Aso Rock Villa, ana fuskantar wannan rashin wuta da ya dabaibaye kusan ko ina a kasar.

A daidai lokacin da ake fama da wannan matsala, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba ya nan. Tun kwanakin baya ya je ganin Likita a kasar Birtaniya.

Kara karanta wannan

Rashin wuta, wahalar mai, ASUU da matsin lamba 6 da ‘Yan Najeriya suka shiga ciki a yau

Wata majiya ta sanar da jaridar cewa da na’urorin bada wutar lantarki ake amfani har a gidan gwamnatin Najeriya, musamman a ‘yan kwanakin bayan nan.

"Haka abin yake ko a nan"

“Mutane su na kuka a kan matsalar wutar lantarki. Haka lamarin yake a fadar shugaban kasa; da janaretoci ake amfani a kullum.” - Majiya.

Kamar yadda majiyar ta shaida, ma’aikatan Julius Berger ne suke samar da man da ake amfani da shi a na’urorin, yanzu haka akwai karanci da tsadar man inji.

Fadar Shugaban kasar Najeriya
Ana taro a fadar Aso Villa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Garba Shehu ya yi gum

Jaridar ta ce ta yi kokarin tuntubar jami’in da ke magana da yawun bakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu domin jin gaskiyar abin da yake faruwa.

Sai dai Malam Shehu ya ki furta komai, ya ce Ministan wutar lantarki ya riga ya yi jawabi.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

Ma'aikata su na kuka

Rahoton ya kuma nuna cewa ma’aikatun gwamnatin tarayya su na zaune ne din-dim a sakamakon tabarbarewar matsalar wutar lantarkin.

Ma’aikata sun gagara yin aiki da kyau, har ta kai wasu su na rufe ofis tun da rana, su tafi gida.

Da aka yi hira da wata ma’aikaciya, ta ce haka suke zaune a cikin duhu a gida da ofis. A dalilin wannan ne wasu su ka daina zuwa wurin aikinsu a Abuja.

Mun kashe kasar nan - Tsohon Minista

Kwanaki tsohon Ambasadan Najeriya zuwa Saudi Arabiya kuma tsohon Minista watau Ibrahim Musa Kazaure ya bayyana cewa su ne suka lalata Najeriya.

Ibrahim Musa Kazaure ya ce abin da suka yi, ya cancanci a daure su. Kazaure ya ce ko kyauta aka ba shi mukami ba zai karba ba saboda ba su taimaki kasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng