Da kudin bashi zamu biya kullin tallafin mai: Ministar kudi ta jaddada

Da kudin bashi zamu biya kullin tallafin mai: Ministar kudi ta jaddada

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za tayi amfani da kudin bashi $2.2 billion da ta karbo don biyan kudin tallafin man fetur.

Gwamnatin tace hakazalika zata karbi wasu basussuka daga bankunan cikin gida don samun biyan kudin tallafin mai a 2022.

Ministar kudi da kasafin kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan yayin hira da Reuters yayin taron hadin kan Larabawa da Afrika dake gudana a birnin Kahira, kasar Masar.

Da kudin bashi zamu biya kullin tallafin mai: Ministar kudi ta jaddada
Da kudin bashi zamu biya kullin tallafin mai: Ministar kudi ta jaddada
Asali: UGC

Zainab ta ce a wannan shekarar, Najeriya ba zata nemi bashin eurobond ba.

A cewarta,

"Tashin da farashin mai keyi a kasuwar duniya babbar matsala ce garemu.... saboda shigo da mai mukeyi kuma hakan na nufin tallafin kudin mai zai cigaba da karuwa"

Kara karanta wannan

Bayan na jiya, wutar Najeriya ta sake lalacewa, Abuja, Legas, da wasu jihohin sun shafu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng