Rikici: An kaure tsakanin sojoji da wasu matasa, an hallaka mutane akalla 6
- An kaure tsakanin sojoji da mazauna wani yanki a jihar Edo, an hallaka mutane akalla 6, inji rahotanni
- Rundunar soji ta karyata cewa ta kai farmaki yankin ne da sunan haya, wanda tuni ta bayyana yadda lamarin yake
- Mazauna yankin sun gana da manema labarai, sun bayyana yadda lamarin mara dadi ya faru a ranar Juma'a
Edo - Rahoto daga jaridar Daily Trust ya ce, an kashe mutane hudu a yankin Obayantor da ke karamar hukumar Ikpoba Okha ta jihar Edo bayan wani rikici da ya barke tsakanin wasu matasa da jami’an sojojin Najeriya.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata a cikin yankin da aka ce suna ganin rigingimun shugabanci bayan tsige shugabansu na matasa (Okhaegele) tare da nada wani sabo.
Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi zargin cewa wani ne ya dauki hayar sojoji ga al’umma da nufin kwato Okhaegele, kuma a lokacin harin an kashe sojoji biyu. Ya ce daga baya sojojin suka kaddamar da harin ramuwar gayya ga al’umma.
Wata majiya daga yankin ta ce sojojin sun zo da yawa inda suka rika harbe-harbe a sama, lamarin da ya tilastawa mutanen tserewa domin tsira da rayukansu. Ya ce an harbe mutane hudu har lahira.
Sai dai mai magana da yawun hedkwatar brigade 4 na rundunar sojin Najeriya, Benin, Yemi Sokoya, ya musanta cewa an yi hayan sojoji zuwa yankin.
Ya kuma yi watsi da labarin kashe sojoji biyu.
A cewarsa:
“Ba a yi hayan sojoji aiki ga al’ummar ba kuma ba a kashe wani soja ba. Ba harin ramuwar gayya ba ne, farmakin an yi shi ne bisa bayanan sirri na tara makamai."
Ya ce sojojin sun kwato wasu bindigogi guda uku, bindigogi kiran AK 47 guda biyu, wata nau'in bindigar guda daya, harsashi 32 da wayoyi.
Sai dai, wani rahoton jaridar Vanguard ya shaida cewa, shida ne aka kashe tare da wani soja daya.
Jami'an tsaro sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane bayan sace matar aure a jigawa
A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani mutum mai shekaru 46 da ake zargi da yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) na rundunar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Dutse ranar Talata.
Shiisu ya ce wanda ake zargin da aka kama a ranar 28 ga watan Fabrairu, ana zargin dan tawagar da suka yi garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara 22, Hadiza Alhaji-Chadi kwanan nan a kauyen Marma.
Asali: Legit.ng