Wutar lantarki ta dauke a Legas, Abuja Kaduna da wasu jihohi gaba daya, kamfanonin lantarki sun bayyana

Wutar lantarki ta dauke a Legas, Abuja Kaduna da wasu jihohi gaba daya, kamfanonin lantarki sun bayyana

Kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya sun bayyana dalilin da ya sa wuta ta dauke a fadin tarayya yau Litinin, 14 ga watan Maris, 2022.

Mazauna Legas, Abuja, Enugu, Kaduna da sauran jihohi sun ce tun da aka dauke wuta har yanzu babu.

Akalla kamfanoni hudu sun saki jawabin tabbatar da hakan a shafukan ra'ayi da sada zumuntarsu.

Sun ce tushen wutan Najeriya gaba daya ne ya lalace misalin karfe 10:40 na safe.

Kamfanin raba wutar Enugu, EEDC, a jawabin da mai magana da yawunsa, Emeka Ezeh,ya saki yace har yanzu suna sauraron martani daga wajen gwamnati don dawo da wutan.

Yace:

"Kamfanin raba wutar Enugu, EEDC, na sanar da kwastamominsa a yankin kudu maso gabas cewa wutar kasar ce ta lalace gaba daya ranar Litinin misalin karfe 10:40 na safe."

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

"Wannan shine dalilin da yasa ake fama da rashin wuta."
Saboda haka dukkan na'urorinmu dake baiwa Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo ba zasu iya aiki ba."

Kamfanin wutar lantarkin Legas Eko Electricity Distribution Company (EKEDC) kuwa yace har yanzu suna tattauna wa da gwamnati don dawo da wuta.

Hakazalika kamfanonin wutan birnin tarayya Abuja da Kaduna sun saki irin jawaban da sauran kamfanonin suka saki

Wutar lantarki ta dauke a Najeriya gaba daya, kamfanonin lantarki sun bayyana
Wutar lantarki ta dauke a Najeriya gaba daya, kamfanonin lantarki sun bayyana
Asali: Facebook

Wutar lantarki ta dauke a Najeriya gaba daya, kamfanonin lantarki sun bayyana
Wutar lantarki ta dauke a Najeriya gaba daya, kamfanonin lantarki sun bayyana
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng