Binciken Mako: Kayan Masarufi uku da suka yi tashin gwaurin zabi a babbar kasuwar Najeriya

Binciken Mako: Kayan Masarufi uku da suka yi tashin gwaurin zabi a babbar kasuwar Najeriya

  • Farashin kayayyakin masarufi a kasuwar jihar Legas na sama suna ƙasa saboda kalubalen tsaro, canjin kudi da sauran su
  • Karancin Man fetur ba ya cikin abubuwan da suka jawo tashin kayan, sai dai yan kasuwa sun ce rashin dai-daiton tattalin arziki ne babban dalili
  • A wannan makon, Legit.ng Hausa ta shiga babbar kasuwar Legas don jin ta bakin yan kasuwa kan kayan masarufin da suka ƙara tsada da masu arha

Lagos - Abubuwan dake faruwa a faɗin duniya na cigaba da shafar kayan masarufi a Najeriya, a cewar yan kasuwa.

A wani bincike da Legit.ng Hausa ta gudanar a wata babbar ƙasuwa a Najeriya, mun gano cewa farashin kayan abinci bashi da tabbas kuma samun su ya kara wahala.

Kamar Wake, Shinkafa da Gari, farashin ya sauka da sama da kashi biyar cikin ɗari yayin da kayan Masarufin da ake cikin kakarsu suka ƙara tashi.

Kara karanta wannan

Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya

Kasuwa a Legas
Manyan kayan abinci uku da farashin su ya yi tashin gwauron zabi a kasuwar Legas Hoto: Eisther Odili
Asali: Twitter

Wani ɗan ƙasuwa, Mista Ugwuanyi, ya bayyana cewa farashin kayayyaki a wannan makon na fama da abubuwan dake faruwa a ƙasar nan yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Duk sanda ƙasa ke fama da wani kalubale a wani bangare, mutane abun ke shafa, haka take faruwa da karancin Fetur yanzu. Bai kamata kayan abinci ya san da wannan matsalar ba amma abun takaicin shi ne lamarin ya shafe shi yanzu."
"Masu aikin kawo kayayyakin suna bukatar Fetur dan yin aikin su kuma ƙarancinsa ya shafi kasuwancin su. Zan ce karancin Fetur bai shafi farashi ba, amma ya rage hada-hada."

Sai dai wani dilan kayan abinci ya yi hannun riga da hangen wancan, yana gani cewa kayan dake cikin kakarsu ana siyar da su a farashin da ya dace.

Ya bayyana cewa wasu yan kasuwa ne kawai suke amfani da wannan damar wajen tsawwalawa mutane.

Kara karanta wannan

Neja: 'Yan Ta'adda Sun Farmaki Kasuwa, Sun Yi Kisa, Sun Sace Mutane Da Kayan Abinci Masu Yawa

A jawabinsa ya ce:

"Farashin kayan abincin da muke cikin kakarsu suna da rahusa, amma wasu yan kasuwa na matsa wa mutane. Domin su samu kudi suke ƙara farashin kuma su bayyana cewa ai kaya sun yi tsada."
"Eh kayayyaki sun yi tsada amma akwai ma su arha. Misali Shinkafa, Wake da Gari, farashin su ya sauka a yan makonnin nan, amma kayan haɗin abinci sun tashi a yanzu, gasar kawo su kasuwa ma ake yi."

Waɗan ne kayan abinci ne suka yi tsada?

Kayan Masarufi
Manyan kayan abinci uku da farashin su ya yi tashin gwauron zabi a kasuwar Legas Hoto: Esther Odili
Asali: UGC

A bayanin wani ɗan kasuwa a cikin wannan kasuwa, Egusi, Ogbono, da Cryfish sun yi tashin gwauron zabi a wannan lokacin.

Abin sha'awar shi ne, baki ɗaya waɗan nan kayayyaki a cikin ƙasar nan ake noma su, amma sun yi tsada, wasu yan kasuwa suna kokawa kan farashin kayayyakin.

"Farashin Egbono, Egusi da Cryfish ya ƙaru a watan nan, wasu mu na shan wahala wajen samun kayan da kuma siyarwa mutane a farashi mai rahusa."

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda mai ya kare

"Idan yau ka zo kasuwa ka siya kayan a wani farashi, duk ranar da ka sake dawowa zaka samu farashin ya ninka biyu. Haka ya ja mana bakin jini domin wasu na ganin muna cutar su ne."

Ya farashin kayan guda uku yake a kasuwa yanzu?

Mutumin ya ƙara da cewa:

"Bokitin Fenti na Egusi da ake siyarwa N1,500 ko N2,000, yanzun ya kai N4,000 zuwa sama, yayin ake siyar da bokitin Ogbono N9,000 zuwa sama.
"Yanzu ana sayar da buhun Egusi N120,000 zuwa sama yayin da a baya bai wuce N75,000 ba. Amma farashin Buhun Ogbono ya kai N115,000 a yanzu, a baya kuma ana siyar da shi N100,000."
"Egusi na cikin kaka, amma farshinsa ya yi wannan tashin bamu san me ya faru ba, amma abun da ke banbanta buhunan abubuwan biyu shi ne yawa. Buhun Egusi ya zarce buhun Egbono yawa, ni kaina ina da buhunan Egbono da yawa."

Kara karanta wannan

Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa

A cewar mutumin ana samun bokiti 16 a buhun Egbono, yayin da Buhun Egusi ke kai wa bokiti 30.

"Farashin Cryfish ya danganta da lokaci da kuma wurin da kasuwa take. Buhun Cryfish kan yi Bokiti 30, rabinsa kuma yana da 15. Ana samun buhunsa kan N50,000 ko N60,000, a baya kuma ba ya wuce N45 000."

Wani abin sha'awa shi ne, ana samun wasu kayan abinci a farashi mai rahusa, misalin su Shinkafa, Wake, Gari da kuma wasu kayan itatuwa.

Ana samun buhun gari daga N12,000 zuwa ƙasa, Shinkafa yar ƙasar waje ba ta wuce N26,000, sai kuma Buhun Wake da farashinsa ke farawa daga N50,000 zuwa sama amma kafin yanzu ya kai N75,000. Shinkafa yar gida kuma tsadarta N20,000 zuwa ƙasa.

Tsadar farashin wasu kayayyaki

Kayan itatuwa kuma suna da tsada amma wasu kuma zaka same su cikin farashi mai sauki Wani ɗan kasuwa ya ce yanayin da ake ciki yanzu ya shafi farashin kayan shekara-shekara.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, rayuka sun salwanta

Mutumin wanda ke kasuwancin saida Ayaba, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa:

"Farashin kayan itace a kasuwa ya yi tsada, Kuɗin kawo su kasuwa ya shafi hada-hadar su a kasuwar Legas. Farashin kaya kamar Lemu, Inibi, Aful, Ayaba da Kwai sun yi tsada, amma Faufau, Abarba, Kankana, Kwakwanba da karas suna da arha."
"Amma ina me tabbatar maka cewa kasuwa ta canza mu kan mu bamu jin daɗi komai ya lalace, riƙe kasuwanci ya yi wahala, haka rayuwa ta yi tsada."

A wani labarin kuma Uwar gida ta danna wa Mijinta wuka har lahira daga zuwa bankwana zai koma dakin Amarya

Tsagwaron kishin mata ya yi sanadin rasuwar wani Mai mata biyu yayin da yake yi wa Uwar gida bankwana zai koma dakin Amarya.

Rahoto ya nuna cewa Uwar gidan mai suna Atika ta daba wa mijinsu wuka har lahira a Mararaba dake jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: